Muhimman Abubuwan Sani 10 dangane da Zaben Gwamnan Jihar Anambra

Muhimman Abubuwan Sani 10 dangane da Zaben Gwamnan Jihar Anambra

  • Jihar Anambra za ta gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban shekarar 2025
  • Gwamna Charles Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA yana neman wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar
  • Mun yi duba kan muhimman abubuwa 10 da suka shafi zaben gwamnan da za a gudanar a jihar da ke yankin Kudu maso Gabas

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Awka, Anambra - Gwamna Charles Chukwuma Soludo na neman wa'adi na biyu a matsayin gwamnan jihar Anambra.

Gwamna mai-ci Charles Chukwuma shi ne dan takarar jam'iyyar APGA mai mulki a jihar.

INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra
Gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra Hoto: @CharlesSoludo
Source: Twitter

Abubuwan sani kan zaben gwamnan Anambra

Legit Hausa ta yi duba kan muhimman abubuwan sani dangane da zaben gwamnan na jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ranar zabe

Zaben gwamnan Anambra zai gudana ne a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025 a fadin jihar.

Kara karanta wannan

INEC ta dauki matasa 24000 aikin zabe, Yiaga ta hango abin da zai faru a Anambra

A sakamakon shari'ar zabe da tsige gwamnoni da aka yi a baya, ba a gudanar da zaben Anambra tare da na sauran jihohi.

2. Yawan ‘yan takara da jam’iyyunsu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da cewa akwai ‘yan takara 16 daga jam’iyyu daban-daban da za su fafata a zaben.

'Yan takarar da INEC ta sanya sunayensu a shafinta na intanet sun hada da:

  • Jeff Nweke - AA
  • John Nwosu - ADC
  • Charles Onyeze - AP
  • Prince Nicholas Ukachukwu - APC
  • Governor Soludo - APGA
  • Echezona Oti - APM
  • Ms. Chioma Ifemeludike - AAC
  • Chukwudubem Nweke - APP
  • Jerry Okeke - BP
  • George Moghalu - LP
  • Geoff Onyejegbu - NNPP
  • Ndidi Olieh - NRM
  • Jude Ezenwafor - PDP
  • Vincent Chukwurah - SDP
  • Paul Chukwuma - YPP
  • Martin Ugwoji - ZLP

3. Jam’iyyar da ke mulki a halin yanzu

Gwamna Chukwuma Soludo shi ne kan madafun ikon jihar Anambra a halin yanzu.

Hakazalika,APGA ce ke mulkin Anambra, ita kadai ce jihar da ka karkashin jam'iyyar da aka kafa a shekarar 2002.

Kara karanta wannan

Abubuwa 8 da ba ku sani ba game da jihar Anambra da ake shirin zaben gwamna

4. Yawan kananan hukumomi

Jihar Anambra tana da kananan hukumomi 21, wadanda aka raba zuwa yankuna uku kuma kowane yake da wakilci a majalisar dattawa.

Yankuna ukun sun hada Anambra ta Arewa Anambra ta Tsakiya da Anambra ta Kudu.

5. Manyan ‘yan takara 4

Ana ganin zaben zai fi zafi a tsakanin:

  • Charles Soludo na APGA
  • Prince Nicholas Ukachukwu na APC
  • George Moghalu na LP
  • Jude Ezenwafor

6. Yawan masu kada kuri’a da PVC

Jaridar Daily Trust ta ce hukumar INEC ta bayyana cewa akwai masu rajista 2,802,790 a jihar.

Daga cikin su, 2,769,137 sun karbi katin PVC dinsu, adadin da ke nuni da kaso 98.8.

Bayanan da aka samu sun nuna karamar hukumar Oyi aka fi samun mutanen da suka karbi PVC da kaso 99.82.

7. Karewar wa’adin Gwamna Soludo

Wa’adin Gwamna Chukwuma Soludo zai kare ne a watan Maris na shekarar 2026.

A zaben shekarar 2021, ya samu kuri’u 112,229, inda ya doke Valentine Ozigbo na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 53,807.

Kara karanta wannan

Daga Obi zuwa Soludo: Yadda APGA ta rike wuta, ta mulki Anambra na tsawon shekaru 20

Gwamna Soludo zai yi takara a zaben gwamnan Anambra
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Source: Facebook

8. Zabe na musamman

Zaben Anambra na bana yana cikin zabubbukan da ake yi a lokacin da bai yi daidai da na kasa gaba ɗaya ba.

Sauran jihohin sun hada da Bayelsa, Osun, Ondo, Edo da Koara. Sai kuma Ekiti da Imo.

9. 'Yan takara mata

Akwai mata biyu da ke neman kujerar gwamna:

  • Ndidi Olieh ta jam'iiyar NRM
  • Chioma Ifemeludike ta jam'iyyar AAC

Haka kuma jam’iyyu shida sun tsayar da mata a matsayin mataimakan ‘yan takara, ciki har da APC, LP, ZLP, APP, BP, da Accord.

10. Sauye-sauye a cikin ‘yan takara

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa jam'iyyar ADC ta gudanar da sabon zaben fidda gwani domin sauya dan takararta.

Hakazalika jam’iyyun Accord, AAC, LP, da NNPP sun sauya mataimakan ‘yan takararsu kafin zaben.

An bada hutu a jihar Anambra

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Anambra ta ayyana ranar hutu domin zaben gwamnan da za a gudanar a jihar a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Zaben 2025: Jerin gwamnonin da suka mulki jihar Anambra daga 1999 zuwa yau

Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Charles Chukwuma Soludo ta ayyana ranar Juma'a a matsayin ranar da babu aiki.

Ta bayyana cewa an bada hutun ne domin ba ma'aikata damar zuwa yankunansu ta yadda za su kada kuri'unsu a zaben gwamnan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng