Zaben 2025: Jerin Gwamnonin da Suka Mulki Jihar Anambra daga 1999 zuwa Yau
Anambra, Nigeria - Yayin da Jihar Anambra ke shirye-shiryen zaben gwamna na 2025, yana da muhimmanci a waiwayi tarihin siyasar wannan jiha da ake kira “Hasken Ƙasa.”
Anambra ta shahara wajen siyasa mai zafi, tara mutane masu ƙarfi, da kuma rikice-rikicen neman mulki daga dawowar mulkin dimokuradiyya zuwa yau.

Source: Facebook
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya gudanar da zaben gwamnana Anambra a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025, kamar yadda This day ta rahoto.
Daga zamanin Mbadinuju zuwa Obiano, Jihar Anambra ta sha fama siyasar ubangida da da rikice-rikice daban-daban a tarihinta na dimokuraɗiyya.
Gwamanonin da Anambra ta yi tun daga 1999, sun yi ta fafutukar kwace ikon siyasa, yaƙi da rashawa da kuma kawo sauyin da zai inganta rayuwar jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan rahoton, Legit Hausa ta zakulo muku gwamnonin da suka mulki jihar Anambra tun daga dawowar dimukuradiyya a 1999 zuwa yanzu. Ga su kamar haka.
1.Chinwoke Mbadinuju (1999–2003)
Chinwoke Mbadinuju shi ne gwamnan farko na farar hula a Jihar Anambra bayan dawowa farar hula daga 29 ga Mayu 1999 zuwa 29 ga Mayu 2003, kamar yadda The Nation ta kawo.
Mulkinsa cike yake tasirin masu hannu da shuni da ubangidan siyasa, musamman dan kasuwa, Emeka Offor, wanda ake ganin shi ya rika juya gwamnatin a hannunsa.
A lokacin mulkinsa na shekaru hudu, jihar Anambra ta fuskanci yajin aiki, rashin biyan albashi, rashin tsaro, da rikice-rikicen siyasa.
Ma’aikata suna shafe watanni ba tare da an biya su albashi ba, yayin da kungiyar Bakassi Boys ta shahara da kai hare-hare, wanda ya bata sunan gwamnati.
Jaridar The Cable ta tattaro cewa a watan Afrilun 2023, Allah ya yi wa tsohon gwamnan, Chinwoke Mbadinuju rasuwa.
2. Chris Ngige (2003–2006)
Dr. Chris Ngige, dan jam’iyyar PDP, ya shugabanci jihar Anambra daga 29 ga Mayu 2003 zuwa 17 ga Maris 2006.

Kara karanta wannan
Daga Obi zuwa Soludo: Yadda APGA ta rike wuta, ta mulki Anambra na tsawon shekaru 20
Bayan hawan Ngige kan kujerar Gwamnan Anambra, ya rikide daga kasancewa mai biyayya ga “iyayen gidansa na siyasa” zuwa ubangidan kansa, ya koma yin gaban kansa, lamarin da ya jawo rikicin siyasa mai zafi a jihar.
A lokacin rigimarsa a ubangidansa a siyasa, Ngige ya fito fili ya yi fatali da bukatar ware Naira miliyan 10 a kowane wata da ake zargin Chris Uba ya nema daga gare shi.
Duk da wannan rigima, Ngige ya samu goyon bayan jama’a saboda jajircewarsa wajen tsabtace gwamnati, ya biya albashin ma'aikata da suka dade suna bi bashi, fansho, sannan ya fara aikin gina tituna a jihar.
A watan Agusta, 2006, Kotun Zaɓe ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Nabaruma ta soke nasarar Ngige a 2003, kamar yadda jaridar Pulse ta ruwaito.
Ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Daukaka Ƙara, amma ta tabbatar da hukuncin da ya aauke shi daga kan mulki a ranar 15 ga Maris 2006, inda aka bai wa Peter Obi na APGA nasara.
3. Peter Obi (2006)
Peter Obi na jam''iyyar APGA ya tsaya takara a zaben 2003 amma ya sha kaye, inda ya garzaya kotu ya kalubalanci sakamakon zaben da INEC ta sanar lokacin.
Bayan kusan shekaru uku yana gwagwarmaya a kotu, an tabbatar da shi a matsayin gwamna a watan Maris, 2006, kamar yadda Vanguard ta kawo a rahotonta.
Bai dade a ofis ba, Majalisar Dokokin Anambra ta tsige shi a watan Nuwamba, 2006. inda mataimakiyarsa, Virginia Etiaba, ta karɓi mulki, hakan ya sanya ta zama mace ta farko da ta zama gwamna a tarihin Najeriya.

Source: Twitter
4. Virginia Etiaba (2006-2007)
Virginia Etiaba ta yi mulki na ɗan lokaci daga 3 ga Nuwamba 2006 zuwa 9 ga Fabrairu 2007, kamar yadda Bussiness Day ta ruwaito.
Da farko ta yi jinkirin karɓar mulki, amma daga baya ta bayyana cewa, “Na amince saboda yanayin da ake ciki na musamman ne. Jihar Anambra na buƙatar kwanciyar hankali.”
Mulkin ta ya ƙare ne bayan Peter Obi ya dawo kan mulki, lokacin da kotun daukaka kara ta soke tsigewar da aka masa.
5. Andy Uba (2007)
Emmanuel Nnamdi (Andy) Uba ya hau karagar mulki a ranar 27 ga Mayu 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, amma kotun koli ta tsige shi bayan kwanaki 14 kacal a ofis.
A rahoton Premium Times, kotun ta yanke hukuncin cewa wa’adin Peter Obi bai ƙare ba, don haka nasarar Andy Uba a zaben 2007 ba ta da inganci.
Wannan takaitaccen lokacin da ya shafe a kan mulki ya zama ɗaya daga cikin manyan labaran siyasa mafi ban mamaki a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
A tarihi, ba a jero Andy Uba a cikin gwamnonin jihar domin a haramtaccen wa'adi ya yi mulki.
6. Peter Obi (2007–2014)
Peter Obi ya koma kan karagar mulki a jihar Anambra daga ranar 9 ga Fabrairu 2007 har zuwa 17 ga Maris 2014.
Salon shugabancinsa ya bambanta da na magabatansa, ya yi kokarin nuna gaskiya, tsari, da maida hankali kan ilimi, gine-ginen ababen more rayuwa.
A zamanin mulkin Obi, Anambra ta samu girmamawa a ƙasa baki ɗaya saboda yadda ya gudanar da mulkinsa da matse bakin aljihu.
Har yanzu ana yaba masa a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin da ba su fuskanci zargin rashawa bayan kammala wa’adinsu ba.
7. Willie Obiano (2014–2022)
Willie Obiano shi ne wanda ya gaji Peter Obi a ranar 17 ga Maris 2014 ƙarƙashin jam’iyyar APGA.
A shekarunsa na farko, mutanen Anambra sun ga alamun cika alƙawari da ci gaba, amma daga baya mulkinsa ya fara fuskantar zarge-zargen rashawa, son kai da rashin tsari a harkar kuɗi.
Masu suka sun zarge shi da barin muhimman ayyukan raya kasa da kuma rashin biyan ma’aikata albashi da fansho da ya kai biliyoyin Naira.
A wani rahoto da Daily Post ta wallafa, duk da kalubalen da Obiano ya fuskanta a lokacin da yake gwamna, ya yi kokarin kawo sauyi da ci gaban al'umma.
8. Charles Chikwuma Soludo
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Farfesa Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra.
Soludo ya ci nasara a kananan hukumomi 19 daga cikin 21 na jihar Anambra, inda ya samu ƙuri’u 112,229, ya doke sauran ‘yan takara a zaben da aka gudanar ranar 6 ga watan Nuwamba, 2021.
Jam'iyyar PDP ta zo ta biyu da ƙuri’u 53,807, jam’iyyar APC ta samu 43,285, sai YPP da ta samu 21,261, kamar yadda BBC News ta rahoto.

Source: Twitter
A halin yanzu, Gwamna Soludo ke mulki a jihar Anambra kuma shi ne dan takarar jam'iyyar APGA a zaben da za a yi ranar Asabar mai zuwa, inda yake neman zango na biyu.
Gwamna Soludo ya ba da hutu a Anambra
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Anambra karkashin Gwamna Charles Chukwuma Soludo, ta ayyana ranar hutu domin zaben gwamnan da za a gudanar.
Gwamnatin ta ayyana ranar Jumma’a a matsayin rana ta hutu ga ma’aikatan gwamnati kafin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar Asabar.
Ta dauki wannan wannan matakin ne da nufin karfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati domin su shiga cikin zaben a dama da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




