Gwamna Ya Gaji da Magana, Ya Warware Zare da Abawa kan Jita Jitar Komawa ADC

Gwamna Ya Gaji da Magana, Ya Warware Zare da Abawa kan Jita Jitar Komawa ADC

  • Gwamnatin jiar Osun ta sake fitowa fili ta yi magana kan jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamna Ademola Adeleke zai bar PDP
  • Gwamnatin ta karyata rahoton da ke cewa Adeleke na tattaunawa da tsohon gwamna Rauf Aregbesola domin shiga jam’iyyar ADC
  • Kakakin gwamnan, Malam Olawale Rasheed, ya bayyana labarin da ƙarya da yan adawa suka ƙirƙira domin biyan bukatar kansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin jihar Osun ta yi magana kan labarin da ake dangantawa da Gwamna Ademola Adeleke game da barin PDP.

Gwamnatin ta bayyana cewa babu wata tattaunawa tsakanin Gwamna Ademola Adeleke da tsohon gwamna Rauf Aregbesola kamar yadda ake yadawa.

Gwamna Adeleke
Gwamna Ademola Adeleke da Rauf Aregbesola na ADC a Najeriya. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Source: Facebook

Kakakin gwamnan, Malam Olawale Rasheed shi ya tabbatar da haka a wata sanarwa da Tribune ta samu a ranar Alhamis 6 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dakatar da sarkin da ake zargi yana daukar nauyin ta'addanci a Akwa Ibom

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Gwamna Adeleke kan 'shirin' komawa PDP

Wannan ba shi ne karon farko da Gwamna Ademola Adeleke ya ke fitar da sanarwa inda yake kore rade-radn da ake yadawa kan cewa zai bar jam'iyyyar PDP mai adawa.

Ko a baya ma, an yi ta yada rade-radin cewa Gwamna Ademola Adeleke zai bi sahun gwamnonin jihohin Enugu da Baylesa wajen ficewa daga PDP.

Sai dai Gwamma Adeleke ya musanta duka rahotanni da ake jingina masa cewa yana shirin barin PDP tare da komawa APC mai mulkin kasa.

Adeleke ya kuma ce rikicin da ke faruwa a PDP zai zama tarihi domin sun fara tattaunawa domin warware duk wani sabani a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

Gwamna Adeleke ya karyata ganawa da Aregbesola domin komawa ADC
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Source: Facebook

Hadimin Gwamna ya karyata labarin komawarsu ADC

Rasheed ya yi martani ne kan kan batun shiga jam’iyyar ADC da aka ce gwamna Adeleke na shirin yi wanda aka yi ta yadawa a kafofin sadarwa, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Diri bayan komawa jam'iyyar APC

Ya ce labarin da ke yawo a wasu kafafen sadarwa ƙarya ne, kuma ya ja hankalin jama’a da su yi watsi da shi gaba ɗaya saboda babu gaskiya ko kadan.

A cewar Rasheed, rahoton da ke cewa Gwamna Adeleke na tattaunawa da sakataren ADC na kasa wata manufa ce daga jam’iyyar adawa domin ta da hankali.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Gwamna Adeleke ba ya tattaunawa da tsohon Gwamna Aregbesola kan ADC, kuma ba shi da wani shiri na shiga jam’iyyar. Jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya.”

Gwamna Adeleke ya cika baki kan zabe

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi tsokaci kan zaben gwamna da za a gudanar a shekarar 2026 mai zuwa idan Allah ya kai mu.

Gwamna Ademola Adeleke ya cika baki da cewa babu wanda zai iya kayar da shi a zaben gwamnan jihar, domin ya yi abin a zo a gani a mulkin da yake yi a Osun.

Adeleke ya nuna cewa a baya ya doke gwamna mai ci inda ya yi nasara a kansa, ballantana kuma yanzu da yake kan madafun iko wanda zai yi wahala ko kusa yan adawa su kamo shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.