Anambra 2025: Dalilai 4 da Za Su Sanya Dan Takarar APGA Ya Lashe Zaben Gwamna

Anambra 2025: Dalilai 4 da Za Su Sanya Dan Takarar APGA Ya Lashe Zaben Gwamna

Anambra — Masu kada kuri'a a jihar Anambra za su fita ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025, domin zaben wanda zai shugabance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rahoton Legit.ng ya nuna cewa wannan zaben ya zama filin gasa tsakanin manyan ‘yan siyasa, jam'iyyu, attajirai, da kungiyoyin siyasa da ke fafutukar tsara makomar Anambra.

Ana hasashen cewa Charles Soludo na jam'iyyar APGA zai iya lashe zaben Anambra
Gwamna Charles Soludo na jam'iyyar APGA lokacin yakin neman zabensa a Anambra. Hoto: @CCSoludo
Source: Facebook

Jimillar ‘yan takara 16 ne ke neman kujerar gwamnan jihar Anambra, ciki har da Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA, kamar yadda rahoton INEC ya nuna.

Anambra: Abubuwan da za su ba APGA nasara

An rahoto cewa kowane dan takara ya gudanar da yakin neman zabensa a dukkan kananan hukumomi, sannan yanzu sun zuba idanuwa don ganin wa jama'a za su zaba.

Kara karanta wannan

Jihohin da APC da PDP ke mulki a Najeriya kafin zaben gwamnan Anambra na 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu manyan dalilai hudu da za su iya sanya wa dan takarar jam'iyyar APGA, Gwamna Charles Soludo ya sake lashe zabe:

1. Fa’idar kasancewa a mulki

Jam’iyyar APGA ce ake ganin tana da mafi girman damar lashe zaben gwamnan Anambra na 2025, in ji rahoton Premium Times.

Gwamna Charles Soludo, wanda ke neman wa’adinsa na biyu, yana samun yabo daga jama’a da dama saboda ya inganta tsaro, da gyara harkar lafiya a jihar.

Masu lura da harkokin siyasa na ganin wannan zai ba shi gagarumin fifiko a kan sauran 'yan takara, duk da dai ita siyasa ba ta da tabbas.

2. Karfi iko da tsarin jam’iyyar APGA

APGA ta nuna karfinta a matakin ƙasa a watan Satumba 2024, lokacin da ta lashe dukkan mukaman shugabancin kananan hukumomi da kansiloli a cikin Anambra.

Wannan nasara ta tabbatar da cewa jam’iyyar tana da karfi mai yawa a cikin jihar, wanda zai taimaka mata sosai a zaben gwamna mai zuwa.

Kara karanta wannan

Trump na neman kawo hari Najeriya, an jibge jami'an tsaro 60000 domin zaben Anambra

Masu lura da harkokin zabe sun ce irin wannan tsarin ne ke bada tabbacin nasara ga jam'iyyun da ke mulki a jihohi.

3. Rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa

Babban abin da zai iya taimakawa APGA shi ne rikicin da ke cikin jam’iyyun adawa kamar LP da kuma PDP.

Wadannan jam’iyyu na fama da rikicin cikin gida da rashin hadin kai, wanda zai sa su kasa shirye-shiryen da za su iya kai su ga nasara kafin ranar zabe.

Wani masani ya ce, idan adawa ta ci gaba a tsakanin jam'iyyun adawa, to ba shakka APGA za ta ci gaba da zama mai rinjaye a Anambra.

4. Tasirin APGA da farin jinin Soludo

A siyasar yankin Kudu maso Gabas, jam’iyyar APGA ta dade tana da irin nata tasiri, inda har wani mai sharhi, Cornel Osigwe, ya bugi kirji da hakan.

A zantawarsa da Arise News, Osigwe ya ce:

"Babu wani dalili da zai sanya APGA ta kasa yin barci saboda wannan zaben, domin kowa ya shaida cewa tana aiki, kuma ta yi nasarar kawo gwamnoni uku, wasu a wa'adin farko wasu a na biyu.

Kara karanta wannan

Ido zai raina fata: An cafke dan takarar NNPP da zargin kai wa Gwamna Bago hari

"Zaben Anambra mai zuwa, APGA za ta sake dawo da gwamna mai ci saboda ya yi kokari, babu wani fanni da bai taba ba, kuma ya kawo ci gaban da kowa ya shaida."

Gwamna Charles Soludo kuma na da siffar jagora mai hangen nesa da jajircewa, lamarin da ya sa wasu ke ganin cewa gwamnan na iya samun tazarce saboda kwarin guiwa da mutunta shi da jama’a ke yi.

INEC ta sanya ranar zaben Anambra

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, watau INEC, ta ce za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Tun a lokacin, hukumar INEC ta bayyana cewa jam'iyyu za su gudanar da zabukan fitar da gwani na daga ranar 20 ga Maris 2025 zuwa 10 ga Afrilu, 2025.

Sannan hukumar ta bude shafin dora bayanan ɗan takara da ƙarfe 9.00 na safiyar ranar 18 ga Afrilu 2025 kuma ta a rufe da ƙarfe 6.00 na yammacin ranar 12 ga Mayu 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com