Abin da Tinubu Ya Gayawa Gwamna Diri bayan Komawa Jam'iyyar APC
- Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sauya sheka zuwa jam'iyyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya
- Douye Diri ya koma jam'iyyar APC ne kwanaki kadan bayan ya sanar da ficewarsa daga PDP mai adawa
- Shugaba Bola Tinubu ya kwararo yabo ga gwamnan kan matakin da ya dauka na shigowa jam'iyya mai mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da shigowar gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, zuwa jam'iyyar APC.
Shugaba Tinubu ya bayyana sauya shekar Gwamna Diri a matsayin alamar ci gaba da hadin kai.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen bikin tarbar Gwamna Diri zuwa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da bikin ne a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamban 2025 a birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan
Daga shiga APC, Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawarin kaso 99 na kuri'u a zaben 2027
Me Tinubu ya gayawa Gwamna Diri?
Shugaba Tinubu ya yabawa salon mulkin Gwamna Diri da jajircewarsa wajen kawo ci gaba a jiharsa.
“Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta wadanda suka yi amanna cewa ci gaba na gaskiya zai tabbata ne idan muka hadu muka yi aiki tare."
"Gwamna Douye Diri, labarinka yana kama da na jama’arka. Ana siyasa ne don ci gaba, ba hayaniya ko adawa ba."
"Muna alfahari da kai kwarai. Ka yanke shawara mai kyau."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasan ya kuma yabawa Gwamna Diri saboda yadda yake inganta zaman lafiya da haɗin kai ta hanyar gina ababen more rayuwa a fadin jihar.
“Ka jagoranci jiharka da kwanciyar hankali da mutunci, sannan tare da jajircewa wajen kawo ci gaba da zaman lafiya."
"Ka gina hanyoyi zuwa kauyuka masu nisa, ka ginawa mutane gada inda da babu, ka kawo haske inda duhu ya mamaye. Wannan shi ne ainihin shugabanci da tausayi."
- Shugaba Bola Tinubu
Gwamna Diri ya samu yabo
Tinubu ya bayyana sauya shekar Gwamna Diri zuwa APC a matsayin komawa gida cikin iyalin masu cigaba.
“Yanzu ka zama wani ɓangare na dangi guda da ke tunani da aiki tare. Muna maraba da kai, kuma za mu tallafa maka kamar yadda ka kasance jarumi tun da farko."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, wanda ya yi jawabi a wajen bikin, ya roki Gwamna Diri da ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027.
Yilwatda ya bayyana Bayelsa a matsayin jiha muhimmiya ga jam’iyyar mai mulki, yana mai kira ga gwamnan da ya karfafa ta a yankin.
Bikin ya ja hankalin dubban magoya bayan APC waɗanda suka rika daga tutoci da raira taken jam’iyyar cikin farin ciki.
Gwamna Diri ya yi wa Tinubu alkawari
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya yi wa Shugaba Bola Tinubu alkawari kan zaben 2027 da ake tunkara.
Sanata Douye Diri, ya yi wa Shugaba Tinubu alkawarin samun kashi 99 cikin 100 na ƙuri’un jihar Bayelsa a zaben 2027.
Hakazalika ya bayyana cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC ne saboda salon yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da mulkin kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

