Tinubu Ya Karbi Yan Majalisa 3 da Wasu Manyan Jiga Jigai da Suka Koma APC a Kaduna

Tinubu Ya Karbi Yan Majalisa 3 da Wasu Manyan Jiga Jigai da Suka Koma APC a Kaduna

  • Shugaba Bola Tinubu ya karbi manyan jiga-jigan siyasar Kudancin Kaduna da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Tinubu ya bayyana cewa sauya shekar da manyan yan siyasa ke yi zuwa APC na nuna yadda jam'iyyar ke kara karbuwa a wurin jama'a
  • Masu sauya shekar, ciki har da yan Majalisa sun ce nasarorin Tinubu da Gwamna Uba Sani ne suka jawo hankalinsu zuwa APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wasu fitattun ‘yan siyasa sama da 10 da suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC a Kudancin Kaduna.

Yan siyasar, wadanda suka hada da yan Majalisar Tarayya da na jiha, sun koma APC ne tare da dubban magoya bayansu.

Taron karbar masu sauya sheka a Kaduna.
Hoton Gwamna Uba Sani, Femi Gbajabiamila da wasu manyan jiga-jigai a wurin taron karbar masu sauya sheka a Kudancin Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Tinubu ya karbi masu sauya sheka

Kara karanta wannan

Sanatan Kaduna, Barista Katung ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Premium Times ta tattaro cewa Tinubu ya karɓi masu sauya shekan ne a taron da aka shirya a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a, a ranar Asabar.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya wakilci Shugaba Tinubu a wurin taron.

Fitattu daga cikin waɗanda suka sauya sheka sun haɗa da Sanata Sunday Katung (PDP–Kaduna ta Kudu), Dan Majalisar Wakilai, Daniel Amos (PDP–Jema’a/Sanga), da Ali Kalat, ɗan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar Jema’a.

Mr. Gbajabiamila ya bayyana cewa sauya shekar ya nuna yadda APC ke samun karɓuwa da amincewa a sassan jihar Kaduna da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ya yaba wa Gwamna Uba Sani saboda irin jagorancinsa na haɗin kai, yana mai kira gare shi da ya ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar APC a jihar.

'APC ta jafa tarihi a kudancin Kaduna'

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, wanda ya halarci taron, ya bayyana lamarin a matsayin tarihi, yana mai an dade ana kallon Kudancin Kadunaa matsayin gida ga PDP.

"Shekaru da dama, suna karbe muku gobe, muradi da kuma fatan da kuke da shi, amma yau wannan ya ƙare, kuma jama’a sun dawo da ikon da ke hannunsu,” in ji Abbas.

Kara karanta wannan

Jiga jigai da 'yan Kwankwasiyya sama da 600 sun watsar da jar hula, sun koma APC a Kano

Shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar haɗin kai, ci gaba da gaskiya.

A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya ce sauya shekar ya bude sabon shafi a siyasar Kudancin Kaduna da ma Najeriya baki ɗaya.

Ya sake jaddada aniyarsa ta gudanar da mulki cikin adalci ga kowane ɓangare na jihar, ba tare da la’akari da bambancin siyasa, kabila ko addini ba.

Gwamna Uba Sani da masu sauya sheka.
Hoton Gwamna Uba Sani tare da manyan yan siyasar da suka dawo APC a Kudancin Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Dalilan yan siyasar na komawa APC

A madadin masu sauya shekan, Sanata Katung da Hon. Amos sun bayyana cewa nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a Kudancin Kaduna ne suka karfafa musu gwiwar shiga APC.

Sun ce sun yi shawarwari da al’ummarsu kafin ɗaukar matakin, kuma jama’a sun ba su goyon baya, kamar yadda tashar Channels ta rahoto.

Sun yi alkawarin amfani da ƙwarewarsu da tasirinsu wajen ƙarfafa jam’iyyar APC a Kudancin Kaduna da ma Najeriya baki ɗaya.

Wani shugaban kungiyar matasan APC a karamar hukumar Kaduna ta Kudu, Zaharadeen Aliyu ya shaidawa Legit Hausa cewa jam'iyyar ta kama ko'ina a Kaduna.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Kotu ta kwace kujerar dan Majalisar Tarayya daga Jihar Zamfara

Matashin ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya kafa gwamnatin da ta jawo kowa a jiki, wanda hakan ya kara jawo hankalin yan siyasa zuwa APC.

"Gwamna Uba Sani ya kafa tarihin karya lagon PDP a Kudancin Kaduna, yanzu APC ta mamaye ko'ina, kuma in sha Allah Tinubu da Uba Sani sai sun yi zango biyu a kan mulki."

Sanata Katung ya bar PDP zuwa APC

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Sunday Katung, mai wakiltar Kaduna ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

A wata sanarwa da ya fitar, dan Majalisar Dattawan ya bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga kudirinsa na yi wa jama'ar mazabarsa hidima.

Ya ce mutanen mazabarsa ne suka bukaci ya hada kai da Shugaba Tinubu da Gwamna Uba Sani, bisa haka ya bar PDP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262