Sanatan Kaduna, Barista Katung Ya Fice daga PDP zuwa Jam'iyyar APC
- Sanata Sunday Katung, mai wakiltar Kaduna ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC
- A wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, Sanata Katung ya ce ya koma APC ne domin amsa kiran mutanen mazabarsa na Kudancin Kaduna
- Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani bisa yadda suka shimfida ayyukan ci gaba a kudancin Kaduna
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Barista Sunday Katung, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, dan Majalisar Dattawan ya bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga kudirinsa na yi wa jama'ar mazabarsa hidima.

Source: Facebook
Channels tv ta ce sauya shekar Sanatan ta zo ne kasa da awanni 24 bayan Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da PDP daga gudanar da babban taronta na kasa na shekarar 2025.

Kara karanta wannan
Jiga jigai da 'yan Kwankwasiyya sama da 600 sun watsar da jar hula, sun koma APC a Kano
Dalilan sauya shekar Sanata Katung
A sanarwar da ya fitar mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Sakon Haɗin Kai da Manufa,” Sanata Katung ya ce sai da ya tuntubi mazabu, shugabannin siyasa, iyalai da abokai kafin yanke shawarar komawa APC.
Ya bayyana matakin a matsayin “mai wahala da ya zama tilas,” yana mai cewa shigarsa APC zai samar da karin ayyukan ci gaba a Kudancin Kaduna.
Sanata Katung ya kara da cewa ya zabi komawa jam'iyyar APC ne domin amsa kiran jama’ar mazabarsa da suka bukaci ya hada kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani.
Sanatan Kudancin Kaduna ya yabi Tinubu
Ya yabawa shugabannin biyu bisa mulkin haɗin kai da ayyukan ci gaba da suka shimfiɗa a yankin, yana mai cewa hakan ya tabbatar da niyyarsu ta samar da adalci da zaman lafiya.
Sanatan ya kuma bayyana cewa shi, tare da abokin aikinsa Hon. Daniel Amos da wasu ’yan siyasa, sun yanke shawarar daidaita tafiyarsu da wannan hangen nesa na sabuwar Najeriya.
Ya jaddada cewa duk da cewa ba kowa zai ji daɗin wannan mataki ba, yana roƙon al'ummar mazabar Kaduna ta Arewa su fahimci kyakkyawar niyyarsa, in ji The Nation.

Source: Facebook
A cewar Sanata Katung, bai kamata hakan ya raba abokai ba, inda ya kawo misalin tsohon Shugaban Amurka, Thomas Jefferson, wanda ya ce “bambancin ra’ayi a siyasa bai kamata ya sa mutum ya rabu da abokinsa ba.”
Katung ya tabbatar da cewa zai ci gaba da kasancewa kusa da jama’arsa, tare da yin aiki kafada da kafada da gwamnatin APC domin kawo ingantaccen shugabanci da ci gaba ga yankin Kaduna ta Kudu.
Yan Majalisa 6 sun bar PDP zuwa APC
A wani labarin, kun ji cewa mambobin Majalisar Wakilai shida daga jihar Enugu sun hada kai sun sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya tabbatar da sauya shekar a wasikun da ya karanta a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun bar tsohuwar jam’iyyarsu ne saboda rikice-rikicen cikin gida da aka gaza warware ba.
Asali: Legit.ng
