Abin Taba Zuciya: Gwamna Ya Zubar da Hawaye a Kasuwa yayin Ganawa da Mata
- Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra yana ci gaba da kamfe yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna
- Farfesa Soludo ya shiga wani yanayi har ya kusa fashewa da kuka bayan wasu tsofaffin ‘yan kasuwa sun ba shi N50,000
- Mata ‘yan kasuwa sun ce sun ba da gudummawar ne saboda ilimi kyauta, kiwon lafiya kyautawa mata da yara a jihar Anambra
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Idemili, Anambra - Gwamnan Anambra, Chukwuma Charles Soludo, ya nuna farin cikinsa bayan kyautar kudin kamfe da mata suka ba shi.
Gwamna Soludo ya shiga wani irin yanayin tausayi har ya kusa kuka a ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, 2025 a cikin kasuwa.

Source: Twitter
A cikin wata tattaunawa da wakilin Legit.ng a yankin, shugabar mata yan kasuwa ta bayyana cewa abin da gwamnan ya musu ba za su manta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya sa Gwamnan Anambra hawaye
Gwamna ya kusa kuka ne lokacin da wasu tsofaffin mata kananan yan kasuwa a karamar hukumar Idemili suka ba shi gudummawar N50,000 domin yakin neman zabe.
Soludo ya kai ziyara zuwa Ojoto a ci gaba da gangamin yakin neman zaben gwamna lokacin da matan suka hau dandalin taro suka ba shi kuɗin a matsayin goyon baya.
Matan sun ce tarihi ba zai yafe musu ba idan suka yi shiru bayan amfana da alherin gwamnati a gare su.
Alkawarin yan kasuwa ga Gwamna Soludo
Matan sun kuma yi alkawarin tallata shi da tursasa iyalansu da abokansu su fito su kada masa kuri’a a ranar zabe.
Soludo, wanda bai boye jin daɗinsa ba, ya gode da cewa:
“Yanzu mutane da kansu suke daukar nauyin kamfen, suna biyan kudi, suna shirya gangami. Wannan ya nuna gwamnati tana aiki, kuma jama’a suna farin ciki.”
Ya ce shekaru huɗu na gaba za su kasance na manyan ayyuka da sauyi mai armashi, sannan Anambra za ta kara canzawa sosai.

Source: Twitter
Dalilin ba Gwamna gudunmawar N50,000
Shugabar mata yan kasuwa, Mrs. Odiuko ta fadawa wakilin Legit.ng jin dadi da kuma dalilin ba gwamnan gudunmawa.
Ta ce:
“Soludo ya ba mu damar samun ilimi kyauta don rage nauyin kudi wajen samun ilimi ga ’ya’yanmu. Haka kuma, muna samun kulawar lafiya ta haihuwa kyauta a asibitocin gwamnati, saboda kokarin gwamnan.
"Don haka, abin da muka bayar bai kai ko kusa da abin da muka riga muka amfana daga gwamnatinsa ba.”
Madam Odiuko, ta ce gudummawarsu ba komai ba ce idan aka kwatanta da abin da gwamnati ta yi musu musamman ilimi kyauta da kiwon lafiya kyauta.
Gwamna Soludo ya musanta shirin kama malamai
Kun ji cewa Gwamnatin Anambra ta yi karin haske kan rade-radin cewa tana shirin kama wasu malaman addinin Kirista.
Gwamna Charles Soludo ya karyata jita-jitar da ke cewa yana kokarin damke malaman addini, musamman Bishof-Bishof na Katolika.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Yan bindiga sama da 80 sun bakunci lahira da suka yi yunkurin shiga Kebbi
Kwamishinan yada labarai, Dr. Law Mefor, ya ce labarin karya ne da aka kirkira domin tayar da hankalin jama’a da bata sunan gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

