"Babu abin da Za Mu Fasa," Jam'iyyar PDP Ta Yi Magana bayan Hukuncin Kotu
- Jam'iyyar PDP ta bayyana aniyarta na gudanar da babban taronta na kasa kamar yadda ta tsara duk da hukuncin kotu
- Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba ya ce jam'iyyar ba ta ji dadin hukuncin kotu da ya hana ta yin taron ba
- Debo Ologunagba ya tuna hukuncin kotun koli na baya-bayan nan, da ya tabbatar da cewa jam’iyya ce ke da ikon gudanar da harkokinta na cikin gida
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar PDP ta ce za ta ci gaba da shirinta na gudanar da babban taro na kasa kamar yadda ta tsara a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025, duk da hukuncin kotu.
Babbar jam'iyyar adawar ta shirya gudanar da wannan taro da za ta zabi sababbin shugabanninta a birnin Ibadan, Jihar Oyo.

Source: Twitter
Wane hukunci kotun ta yanke?
Sai dai babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da taron bayan zargin cewa jam’iyyar ta karya dokokinta, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’a James Omotosho, wanda ke jagorantar shari’ar, ya kuma haramta wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) karɓa, wallafa ko amincewa da sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkan ka’idojin doka da kundinta.
Jam'iyyar PDP ta dage taronta na kasa?
Sai dai a wata sanarwa da kakakin PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar da yammacin Juma’a, jam'iyyar ba za ta dakatar da shirye-shiryenta ba.
“Jam’iyyar PDP ba ta ji dadin hukuncin da kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin Mai shari’a Kolawole Omotosho ta yanke ba, wannan cin mutunci ne ga tsarin dimokuraɗiyya a ƙasarmu."
PDP ta ce hukuncin ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na zaben mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na kasa ba.
“Mun lura da hukuncin kotun koli na baya-bayan nan wanda ya tabbatar da cewa jam’iyya ce ke da ikon gudanar da harkokinta na cikin gida,” in ji Ologunagba.

Source: Facebook
Shin PDP za ta daukaka kara zuwa gaba?
Kakakin ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta daukaka kara a kan hukuncin kotun, domin kare dimokuraɗiyya da tabbatar da tsarin doka a Najeriya.
A rahoton Leadership, Ologunagba ya ce:
“A matsayin jam’iyyar da ke mutunta doka, PDP ta umurci lauyoyinta da su dauki matakin gaggawa na daukaka kara domin tabbatar da ci gaba da tafiyar dimokuraɗiyya mai inganci a kasar nan."
Sule Lamido ya fara shirin maka PDP a kotu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya fara yunkurin shigar da kara kotu kan hana shi tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar PDP.
Rahotanni sun bayyana cewa Sule Lamido ya gana da lauyoyinsa a ranar Talata da ta gabata, kuma ya rattaba hannu a kan takardar da ake sa ran za a mika a gaban babbar kotun tarayya.
Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya sha alwashin neman hakkinsa a kotu sakamakon hana shi fam din shiga cikin yan takarar kujerar shugaban PDP na kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


