Saura Kiris: Gwamna Ya Fadi dalilin Shirin Komawa APC, Ya Samu Goyon Bayan Manya
- An tabbatar da cewa Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba na dab da barin PDP zuwa APC bayan tattaunawa ta sirri
- Kefas ya gana da matasan APC daga kananan hukumomi 16, inda ya ce Taraba ba za ta ci gaba da zama gefe a siyasar kasa ba
- Manyan ‘yan siyasa da magoya baya sun ce matakin zai canza siyasar Taraba, tare da goyon bayan T.Y. Danjuma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sababbin bayanai sun bayyana cewa shirin Gwamna Agbu Kefas na Taraba na barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar AP.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa shirin komawa jam'iyya mai mulki ya kusa kammala, bayan jerin tattaunawa da ganawar sirri a Abuja.

Source: Facebook
Shiri ya kammala domin komawar Kefas APC
Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa gwamnan ya gana da matasan APC, ana cewa ya tabbatar musu da cewa zai koma jam’iyyar nan ba da dadewa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi taron ne a ranar Laraba 29 ga watan Oktobar 2025 a gidan T.Y Danjuma da ke Asokoro, a birnin Abuja.
Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Kwamred Abubakar Gembu tare da wakilan matasan APC daga ƙananan hukumomi 16 na jihar.
Kafin wannan taron, Gwamna Kefas ya tura tawagar magoya bayansa zuwa dukkan kananan hukumomi domin tattauna shawarar sauya sheka.
Sanata Dahiru Bako ya jagoranci tawagar, kuma yawancin wadanda aka tuntuba sun amince da matakin, ciki har da mambobin PDP.

Source: Twitter
Kalaman Gwamna Kefas kan komawa APC
A taron Abuja, Kefas ya shaida cewa jihar Taraba ba za ta cigaba da zama gefe daga siyasar ƙasa ba, cewar rahoton Punch.
Ya ce yana shirin shiga jam'iyyar APC ne don kawo ci gaba, inganta tsaro, da samun kulawar gwamnatin tarayya.
Matasan APC sun yaba da matakin gwamnan, suna kiran shi jarumi mai hangen nesa wanda ya zabi amfanin al’ummar Taraba sama da jam’iyya.

Kara karanta wannan
APC ta jero sunayen gwamnan Filato da gwamnoni 3 da za su sauya sheka kafin karshen 2025
Shirin shiga APC na gwamnan ya ja hankalin ‘yan siyasa, inda ake kallon hakan a matsayin matakin da zai canza taswirar siyasar Taraba tun daga 2015.
Shugaban APC a Taraba ya yi magana
Shugaban APC na jihar, Ibrahim El-Sudi, ya ce matakin babbar dama ce, yana mai tabbatar da cewa shigar gwamnan ba zai cutar da tsofaffin ‘yan jam’iyya ba.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Gwamna Kefas ya samu amincewar mai gidansa, Janar T.Y. Danjuma mai ritaya, sannan ya gana da Shugaba Tinubu domin kammala shirin.
Wasu manyan PDP sun ce ‘yan siyasa sun fara neman matsayi domin 2027, saboda Kefas zai zama jagoran APC a Taraba idan ya koma.
Wani dan APC ya tattauna da Legit Hausa
Wani tsohon dan PDP a jihar, Mohammed Abdurrahman ya ce tuni suka koma APC inda suke jiran shigowar gwamna.
Ya ce:
"Mun dade da barin PDP zuwa APC amma mun zo ne domin jiran gwamna Agbu Kefas ya taho ya same mu."
Sauya sheka: Hadimin Gwamna Kefas ya magantu
An ji cewa Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas zai fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya domin samar da ci gaba ga al'ummarsa.
Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Josiah Kente, ya bukaci masu ruwa da tsaki a Taraba su marawa wannan mataki baya.
Ya ce Gwamna Kefas zai koma APC ne ba don son rai ko wata riba da zai samu ba, sai don samar da ci gaba daga gwamnatin tarayya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
