Duk da Rikicin PDP, Gwamna Adeleke Ya Cika Baki kan Zaben 2026

Duk da Rikicin PDP, Gwamna Adeleke Ya Cika Baki kan Zaben 2026

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi tsokaci kan zaben gwamna da za a gudanar a shekarar 2026 mai zuwa
  • Ademola Adeleke ya cika baki da cewa babu wanda zai iya kayar da shi a zaben gwamnan jihar, domin ya yi abin a zo a gani a mulki
  • Gwamnan ya nuna cewa a baya ya doke gwamna mai ci wajen samun nasara, ballantana kuma yanzu da yake kan madafun iko

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya bayyana cewa babu wanda zai iya doke shi a zaben gwamna mai zuwa na ranar, 8 ga watan Agustan 2026.

Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa ba ya jin tsoron “ikon gwamnatin tarayya” a zaben.

Gwamna Adeleke ya hango nasararsa a zaben 2026
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun Hoto: Senator Ademola Adeleke
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Abuja bayan ya gana da kwamitin tantance ‘yan takarar gwamnan Osun na PDP.

Kara karanta wannan

APC ta jero sunayen gwamnan Filato da gwamnoni 3 da za su sauya sheka kafin karshen 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Adeleke ya ce kan zaben gwamnan Osun?

Gwamna Adeleke ya ce yana da cikakken tabbaci cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai yi wani abu da zai bata gwamnatinsa ba.

“Na doke gwamna mai ci a baya domin na hau mulki. Don haka wannan zabe mai zuwa ai wasa ne kawai, zamu yi rawa da murna."

- Gwamna Ademola Adeleke

Gwamnan ya kara da cewa babu wani rikici a jam’iyyar PDP a jihar Osun.

"A Osun, PDP na kan fada. Muna jam’iyya ɗaya, muna aiki tare, babu wani rikici a tsakaninmu."

- Gwamna Ademola Adeleke

Gwamna Adeleke ya jaddada cewa aikin da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru biyu ya isa ya tabbatar masa da nasara a zaben.

“Na kafa tsarin bincike na gaskiya. Duk wanda bai yarda ba, ya duba a intanet ya gani, aikin da muke yi a Osun ya zarce abin da ake tsammani."

Kara karanta wannan

Mutanen birnin tarayya za su zauna a duhu, TCN ya fadi dalilin dauke wuta a Abuja

“"Ina da cikakken kwarin gwiwar cewa zan yi nasara. Na kayar da gwamnan da ke kan kujera kuma yanzu ni ne gwamna. A cikin shekara biyu mun samu nasarori. Ina da kwarin gwiwar cewa babu wanda zai iya nasara a kaina."

- Gwamna Ademola Adeleke

Gwamnan Osun ya fadi abin da zai yi

Da aka tambaye shi abin da zai kara yi idan aka sake zabarsa, Adeleke ya amsa da cewa:

“A wannan karo, kowa zai ji dadi a fadin jihar Osun. Za mu yi rawa, za mu yi aiki.”
Gwamna Adeleke ya cika baki kan zaben 2026
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

Ya kuma bayyana cewa bai tsoron duk wata dabara da za a yi, a hana shi nasara a zaben.

“Ta ya ya zan ji tsoro? Ni sananne ne sosai. Kowa yana sona. A duk inda na je, ko a jam’iyyar APC ma, ina da abokai da yawa. Idan kai mai aiki ne, ba ka jin tsoro. Idan jama’arka suna tare da kai, babu abin da zai firgita ka."

- Gwamna Ademola Adeleke

Gwamna Kefas ya magantu kan komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya tabbatar da batun komawa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa ya gayawa Mai girma Bola Tinubu aniyarsa ta komawa jam'iyyar APC mai mulki.

Ya bayyana cewa shugaban kasa ya mika shi hannun shugaban APC na kasa domin ci gaba da kammala shirin tarbarsa zuwa cikin jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng