Hotunan ’Yar Takarar Gwamna Sun Jijjiga Kafar Sadarwa, Ta Bayyana Surar Jikinta
- ‘Yar takarar gwamna a jam'iyyar AAC a zaben Anambra ta jawo hankalin jama’a bayan sakin hotuna da bidiyon kamfen
- Chioma Ifemeludike ta ce kyau da hankali na iya tafiya tare, ta kuma bayyana cewa tana da kwarewa da karfi don fafatawa
- Ifemeludike ta kira ‘yan Anambra da su guji sayar kuri’a da cin hanci, su zabi shugaba nagari mai gaskiya da tausayin mutane
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Mutane da dama sun yi rubdugu kan yar takarar gwamna a jihar Anambra kan sakin wasu zafafan hotuna.
‘Yar takarar jam’iyyar AAC a zaben Anambra, Chioma Ifemeludike, ta jawo hankalin jama’a a yanar gizo bayan ta saki hotuna da bidiyon kamfen.

Source: Twitter
'Yar takarar gwamna ta yi alfahari gabanin zabe
A shafinta na X a ranar Talata 28 ga watan Oktobar 2025, Ifemeludike ta ce tana alfahari da kasancewarta ‘yar takarar AAC, tana mai cewa ita ce mafi cancanta a zaben 8 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni suka ce Ifemeludike ta ce shugabanci na kowa da kowa ne tana kuma kalubalantar tunanin cewa siyasa mallakar maza ce.
Ta ce lokaci ya yi da mata za su jagoranci sauyi a jihar Anambra bayan kwashe shekaru da dama da maza suka yi.
Sai dai bayan hotunan da wallafa, jama’a sun bambanta a ra’ayi, wasu suna ganin ta makara wajen yakin zabe, wasu kuma suna cewa “siyasa ba rigar kwalliya ba ce.”
Amma wasu da dama sun nuna goyon baya, suna cewa tana wakiltar mata a siyasa da neman kawo sauyi a jihar.

Source: Original
Shawarar da yar takarar gwamna ta ba al'umma
Har ila yau, Chioma ta ce jama’a kar su bari a rude su, ta jaddada cewa mace na iya kasancewa mai kyau da kuma hankali lokaci guda.
Ta kara da cewa neman sauyi da adalci ne ginshikin kamfen dinta wanda zai kawo sauki ga al'ummar Anambra.
Ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a siyasar Najeriya saboda zama mace, tana mai cewa karkatar da tunani ga maza kawai ya daɗe yana hana cigaban al’umma.
Ta ce:
“A Anambra da dama har yanzu suna cewa mace ba za ta iya rike jiha ba, saboda kawai mace ce. Amma ni ba zan ja da baya ba.”
Ifemeludike ta ce batun bai tsaya kan mace ko namiji ba, abin ya shafi cancanta da nagarta da gaskiya ne, ta bukaci mutane su kaurace wa cin hanci, sayen kuri’a da tashin hankali.
Yar takarar gwamna ta yi alkawari ga ma'aikata
Mun ba ku labarin cewa daya daga cikin 'yan takarar gwamna a Anambra ta fito ta gayawa mutanen jihar irin alheri da ta shirya musu idan har ta yi nasara.
Chioma Ifemeludike ta jam'iyyar AAC ta dauki alkawarin inganta jin dadin ma'aikata ta hanyar kara musu mafi karancin albashi zuwa N100,000.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 8 ga watan Nuwambar 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
