Kano: 'Yar APC Ta Cire Mayafin Hamayya, Ta Ce ba Su Taba Gwamna kamar Abba ba
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu yabo daga 'yar adawa bisa ayyukan cigaba da ta ce ya kawo yankinta
- Badariyya Garko, wacce 'yar jam'iyyar adawa ce a Kano ta yabi gwamnatin NNPP da ta ce an dade ba a samu irinta ba a jihar
- Tuni masoya gwamnatin Kano suka fara jinjina mata, inda ake ganin ta yi abu mai kyau tun da siyasa ba ta rufe mata ido ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Daya daga cikin mata 'yan siyasar adawa a Kano, Badariyya Garko ta bayyana ra'ayinta a kan salon mulkin gwamna Abba Kabir Yusuf a jihar.
Duk da cewa 'yar jam'iyyar hamayya ce ta APC, Badariyya ta kwararo yabo ga yadda Gwamna Abba Gida Gida, inda ta ce yana kawo masu ayyukan cigaba.

Kara karanta wannan
Ba yan ta'adda ba ne: Yan sandan Jigawa sun wanke mutanen da suka shigo da makamai

Source: Facebook
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, Badariyya wacce ta bayyana cewa yankinta na Garko a jihar Kano ya jima rabonsa da jagoranci irin na Abba Kabir Yusuf.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: 'Yar adawa ta yabi gwamnatin Abba
A sakonta, Badariyya Garko ta bayyana cewa tun daga shekarar 1999 zuwa yau, ba a samu gwamna da ya yi abin da Abba Kabir Yusuf ke yi ba.
Ta wallafa cewa:
"Wallahi, daga shekara ta 1999 zuwa yau, ba kasafai ake ganin gwamna ko mataimaki a karamar hukumar Garko da yayi aiki irin na Injiniya Abba Kabir Yusif ba."
Badariyya ta kara da jero wasu daga cikin ayyukan Mai girma Abba a Garko:
"Jama’a sun yaba matuka da yadda gwamnan ya gyara asibitin Garko, ya shimfida hanyoyi, ya gyara kasuwa da makarantu. Wasu daga cikin mazauna garin sun bayyana cewa abubuwan da gwamnan ya yi sun kawo sauyi mai ma’ana, kuma sun kawo albarka a rayuwar al’umma.'
Jama'a sun taya Badariyya yabon Abba
Wasu daga cikin masu bibiyar 'yar siyasar a sahar Facebook sun yi sharhi a kan sakon da ta wallafa na yabon gwamnatin adawa.

Source: Facebook
Babangida S. Sani ya ce:
“Hala Ganduje da su Kwamanda ba su taɓa yin abin da ɗan adawa zai yaba masu ba a shekaru takwas ba ko."
Aminu Bin Muallim ya ce:
Abin da su ba za su iya ba kullun muna gaya musu ba zage zage ba ne siyasa adalci shi ne siyasa."
Allahu ya saka miki da alkairi badariyya kin cika gwarziya kin ci kaya a tafiyar apc
Rahama Adam ta ce:
“Ai gaskiya in tazo ka fadet a akan kowa, ko da mahaifinka ne, Masha Allah.”
Abdullahi Salisu ya ce:
"Allah Ya saka miki da alkairi hakan ya nuna mana ke cikkakkiyar yar kishin Garko ce ba makauniyyar adawa ki ke ba. Ki na son garinki gashi kin fito kin godewa Gwamna akan abinda ya yiwa garinki."
Injiniyoyi sun ga kokarin Abba Gida Gida
A baya, kun samu labarin cewa kungiyar injiniyoyi ta NICE ta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf lambar yabo ta musamman saboda yadda ya ke jagorantar cigaban ginin kasa a Jihar Kano.
Shugaban NICE na ƙasa, Otunba Ajanaku, ya mika wannan yabo ga gwamnan a madadin ƙungiyar, inda ya ce suna sane da yadda gwamnan ke ayyuka masu inganci a Kano.
A cikin jawabin da aka gabatar, Ajanaku ya bayyana gwamnan Abba a matsayin shugaba mai hangen nesa, wanda ya maida hankalinsa ga ayyukan more rayuwa ga mazauna jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

