Akpabio Ya Gano Matsalar da Ke Hana Mata Lashe Zabe a Najeriya
- Mata na fuskantar matsalar rashin samun nasara a zabubbukan da ake gudanarwa a Najeriya idan sun fito takara
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga wajen su kansu matan
- Akpabio ya bayyana cewa idan lokacin zabe ya zo, mata na gwammacewa su zabi maza maimakon yan uwansu mata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi magana kan dalilin da ya sa mata ba sa yin nasara a zabubbuka.
Sanata Godswill Akpabio ya danganta rashin nasarar ‘yan siyasa mata a zabubbukan kasar nan da rashin goyon baya daga mata ‘yan uwansu.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin wata babbar tawaga daga kwamitin harkokin wajen majalisar tarayyar Turai (EU).

Kara karanta wannan
Bayan karbar bukatar Tinubu, majalisa ta sa lokacin tantance sababbin hafsoshin tsaro
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An karbi bakuncin tawagar ne da ke karkashin jagorancin Mr. David McAllister, a majalisar dokoki ta kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Meyasa mata ba sa lashe zabe a Najeriya?
"Mata sau da yawa suna kada kuri’a ga maza, wanda hakan ke sa mata masu neman kujeru su kasa samun nasara a zabe.”
- Godswill Akpabio
Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya nuna damuwa kan rashin daidaito tsakanin jinsin mata da maza a harkokin siyasar Najeriya.
Akpabio ya bayyana cewa duk da cewa mata su ne kusan rabin masu kada kuri’a a kasar nan, wakilcin da suke da shi a majalisa na daga cikin mafi karanci a nahiyar Afirka.
A halin yanzu, daga cikin Sanatoci 109 da ake da su, mata guda huɗu kacal yayin da ake da mata 17 daga cikin ‘yan majalisar wakilai 360.
Sai dai Akpabio ya bayyana cewa majalisar dokoki ta kasa na nazarin sababbin hanyoyi da gyaran kundin tsarin mulki domin kara yawan wakilcin mata a siyasa da shugabanci, jaridar Tribune ta tabbatar da labarin.
Ya kara da cewa majalisar ta buɗe kofa don yin aiki tare da kungiyoyin fafutuka kamar Black Women’s Forum domin cin ma wannan buri.

Source: Twitter
EU za ta yi hadin gwiwa da Najeriya
A nasa ɓangaren, McAllister wanda ya jagoranci tawagar EU tare da Jakadiya Greta Mylott, ya ce manufarsu ita ce zurfafa fahimtar halin da ake ciki a Yammacin Afirka da kuma karfafa haɗin gwiwa da Najeriya.
Ya sake jaddada kudurin tarayyar Turai (EU) na tallafa wa kokarin ci gaban dimokuraɗiyya da tattalin arzikin Najeriya, musamman wajen yaki da ta’addanci, sauyin yanayi da matsalolin tattalin arziki.
“EU ta kuduri aniyar tallafawa kokarin ci gaban Najeriya "
- Mr. David McAllister
Sarakuna sun shiga lamarin Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar sarakunan jihar Akwa Ibom, ta shiga lamarin zarge-zargen da ake yi wa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Majalisar sarakunan ta bukaci Patience Akpabio, ‘yar uwar matar Godswill Akpabio, da mijinta Ibanga Akpabio, su kawo kansu a gaban ta.
Ana dai tuhumar Patience Akpabio ne kan wasu kalaman batanci da ta wallafa a kafafen sada zumunta da ke zargin shugaban majalisar dattawan da kashe-kashe a lokacin da yake gwamna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
