PDP Ta Samu Koma Baya a Zamfara, Dan Majalisarta Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Jam'iyyar PDP mai-ci ta gamu da koma baya bayan daya daga cikin 'yan majalisar da take da su ya sauya sheka zuwa APC a jihar Zamfara
- Dan majalisa mai wakiltar Maradun II a majalisar dokokin jihar Zamfara, Maharazu Faru, ya raba gari da PDP wadda ya lashe zabe a karkashinta
- Hon. Faru ya bayyana cewa gazawar Gwamna Dauda Lawal wajen cika alkawuran da ya dauka, na daga cikin dalilansa na ficewa daga PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Maradun II, Maharazu Faru ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
An karɓe shi a hukumance cikin jam’iyyar APC ta jihar Zamfara a wani biki da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.

Source: Facebook
Maharazu Faru ya sanar da sauya shekar tasa ne cikin wata wasika da ya aika ga majalisar dokokin jihar Zamfara ta hannun sakataren majalisar a ranar 27 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: 'yan ta'adda da masu zanga zanga sun yi barazanar kai hari Majalisar Tarayya
Meyasa dan majalisar ya fice daga PDP?
A cikin wasikar, ya bayyana cewa rashin shugabanci nagari a PDP, musamman a matakin jihar, shi ne babban dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar.
“Bayan nazari mai zurfi kan abubuwan da ke faruwa a PDP, musamman a matakin kasa, da kuma ra’ayina kan yadda shugabancin jam’iyyar ke tafiya a Zamfara, na yanke shawarar cewa daga yau ba ni ɗan PDP ba ne, na koma APC."
- Maharazu Faru
Ya kara da cewa, shawarar da ya ɗauka ta biyo bayan tattaunawa da jama’ar mazabarsa, waɗanda suka amince da ya shiga APC.
An karɓe shi tare da daruruwan magoya bayansa a ofishin APC na jiha a Gusau, yayin wani biki da ya samu halartar shugaban jam’iyyar na Zamfara, Hon. Tukur Umar Danfulani, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.
Jagororin PDP sun koma APC a Zamfara
A yayin bikin, wasu shugabannin PDP guda biyar na mazabun Faru/Magami, Gidan Goga, Tsibiri, Kaya, da Janbako, tare da Alhaji Salisu Dodo Faru, wanda shi ne tsohon jami’in PDP na karamar hukumar Maradun, su ma sun sauya sheƙa zuwa APC.

Source: Twitter
A jawabinsa, Maharazu Faru ya bayyana cewa dalilinsa na barin PDP ya samo asali ne daga gazawar Gwamna Dauda Lawal wajen cika alkawuran da ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe musamman game da tsaro.
“Gwamnatin Dauda ba ta nuna adalci ba. Sai waɗanda suke kusa da shi da ƴan jam’iyyarsa kaɗai ke cin gajiyar mulkin. Ana wulakanta mu da nuna mana wariya."
- Maharazu Faru
APC ta tsayar da dan takara a zaben Ekiti
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta tsayar da dan takara a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar a shekarar 2026.
Jam'iyyar APC ta zabi Gwamna Biodun Oyebanji a matsayin dan takararta a zaben wanda za a gudanar a watan Yunin 2026.
Gwamna Biodun Oyebanji Oyebanji, wanda shi ne kaɗai ɗan takara a zaben fitar da gwanin, ya samu kuri’un deleget 885, mutum biyar daga kowace mazaba daga cikin mazabu 177 na jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
