Shugabar LP Ta Kasa Ta Samu Mukami a Jam'iyyar Hadaka, ADC Ta Yi Nade Nade 2 a Kaduna
- Jam'iyyar ADC ta fara gyare-gyare a bangaren shugabancinta a jihar Kaduna domin tunkarar babban zaben 2027 cikin hadin kai
- An nada tsohuwar Ministar Kudi, Sanata Nenadi Usman a matsayin shugabar jam'iyyar hadaka ta Kaduna
- Mataimakin shugaban ADC (Arewa maso Yamma), Malam Jafaru Sani ya zargi APC da kokarin raba kan shugabannin adawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Najeriya – ADC ta bayyana nadin Sanata Nenadi Usman, tsohuwar Ministar Kudi, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a Jihar Kaduna.
Haka kuma, ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na jihar, Alhaji Bashir Sa’idu, a matsayin mai taimakawa shugaban jam'iyyar hadakar watau ADC.

Source: Twitter
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa maso Yamma), Malam Ja’afaru Sani, ne ya bayyana hakan a wani taro a Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabar LP ta samu mukami a ADC
Ya ce jam’iyyar ADC na aiki don haɗa kan shugabannin adawa a jihar ƙarƙashin dandali guda, domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da samun cikakken wakilci na siyasa.
Sanata Nenadi Usman dai ita ce shugabar jam'iyyar LP ta kasa ta rikon kwarya, duk da dai wasu bangarori a jam'iyyar ba su yarda da jagorancinta ba.
Sai dai Malam Ja'afaru Sani ya ce shugabannin hadaka sun kuduri aniyar farfado da ADC tare da gina haɗin kai tsakanin ‘yan kasa domin kawo ƙarshen “mulkin danniya na APC a jihar da ƙasa baki ɗaya.”
"A matsayin wani ɓangare na manufofin samar da shugabanci mai ɗa’a a Kaduna, muna tabbatar da Sanata Nenadi Usman da Muhammad Bashir Sa’idu a matsayin Shugabar da Mataimakin Shugabar ADC a jihar.
"Wannan mataki ne da zai zama tubalin ayyukan hadakar da kuma sake fasalin jam’iyyar ADC a Kaduna,” in ji Ja’afaru Sani.
ADC ta zargi APC da rikita yan adawa
Ya zargi jam’iyyar APC da ƙoƙarin shiga cikin jam’iyyun adawa don tarwatsa haɗin kansu, amma ya jaddada cewa ADC ba za ta bari hakan ya yi nasara ba.
A rahoton Daily Post, Ja'afaru Sani ya ce:
“Mun lura cewa a wannan yunƙuri na lalata haɗin kan shugabannin adawa, wasu ‘yan siyasa da ake amfani da su sun ɗauki matakin shigar da ƙarar kotu a kan wasu shugabannin hadaka ciki har da Mallam Nasir El-Rufai da ni kaina, Ja’afaru Sani."
Ya ƙara da cewa shugabannin hadaka sun yanke shawarar kora da sanya takunkumi kan mambobin da suka shigar da ƙarar wasu manyan jagororin ADC a matakin ƙasa.

Source: Twitter
An kona sakatariyar ADC a Ekiti
A wani labarin, kun ji cewa miyagu da ke zargin yan dabar siyasa ne sun kona ofishin jam’iyyar ADC da suka kai kai hari a ranar da ake shirin rantsar da sababbin shugabanni a Ekiti.
Wannan lamari ya faru ne yayin da ake shirin fara taron rantsar da shugabannin ADC na jihar Ekiti, inda ‘yan daba suka kai hari suka kona rumfuna da kujeru.
Rahotanni sun nuna cewa abubuwan da suka lalace sun hada da rumfuna 1000 da ke dauke da kujeru, da wasu sassan ginin da suka kama da wuta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

