APC Ta Tanka da Gwamna Muftwang Ya Ce Ana Matsa Masa Lamba Ya Koma Jam'iyyar

APC Ta Tanka da Gwamna Muftwang Ya Ce Ana Matsa Masa Lamba Ya Koma Jam'iyyar

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya fito ya bayyana cewa yana fuskantar matsin lamba don ya koma jam'iyyar APC
  • Caleb Mutfwang ya bayyana cewa wasu manyan 'yan siyasa a Plateau sun taso shi a gaba kan sai ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP
  • Sai dai, jam'iyyar APC mai mulkin kasa ta kalubalanci gwamnan cewa ya bayyana mutanen da ke huro masa wuta ya shigo cikinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Jam’iyyar APC a jihar Plateau ta yi martani kan ikirarin da Gwamna Caleb Mutfwang ya yi na cewa ana matsa masa lamba ya koma jam'iyyar.

Jam'iyyar ta yi watsi da ikirarin na gwamnan wanda ke cewa wasu jiga-jigan 'yan siyasa da ke jihar suna matsa masa lamba ya fice daga PDP zuwa APC.

APC ta yi wa gwamnan Plateau martani
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda da Gwamna Caleb Mutfwang Hoto: Prof Nentawe Yilwatda, Caleb Mutfwang
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar APC a Plateau, Shitu Bamaiyi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Gwamna Mutfwang ya fadi matsayarsa bayan fuskantar matsin lambar ya koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutfwang na fuskantar matsin lamba

A karshen mako da ya gabata, Gwamna Mutfwang ya shaida wa mahalarta wani taro a gidan gwamnati da ke Jos cewa wasu ‘yan APC na kokarin jawo shi zuwa jam’iyyarsu.

Amma gwamnan ya jaddada cewa Allah ne kadai da mutanen da suka kada masa kuri'a za su iya sanyawa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Wasu kungiyoyin APC, ciki har da North Central APC Forum karkashin jagorancin Saleh Zazzaga, sun dade suna kira ga gwamnan da ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki.

Sai dai, kwanan nan wasu jiga-jigan APC a jihar Plateau suka kada kuri’ar kin amincewa da shigowarsa, suna cewa “ba sa bukatarsa” a cikin jam’iyyar.

Wane martani jam'iyyar APC ta yi?

Da yake mayar da martani ga furucin gwamnan, mataimakin mai magana da yawun APC na jihar Plateau, Shittu Bamaiyi, ya bayyana cewa Mutfwang yana gayawa kansa karya ne kawai kamar yadda aka gani a rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu murus": Nyesom Wike ya fadi masu laifin kashe jam'iyyar adawa

APC ta kalubalanci Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Ya bayyana cewa da gwamnan ya yi abin da ya dace kan mulkin jihar, da ba a rika batun sauya shekarsa ba.

“Idan har yana nufin alheri ga magoya bayansa da jiharsa, ya kamata ya fito fili ya bayyana sunayen wadanda ke matsa masa lamba da kuma dalilin hakan."
“Ko ma dai menene, babban abin kunya ne ga gwamna mai ci idan jam’iyyar adawa ta fito fili ta ki karɓarsa, alhali manufarta ita ce ta lashe zaɓe a gaba."

- Shittu Bamaiyi

Shittu Bamaiyi ya kuma yi nuni da cewa irin wannan furuci daga Gwamna Mutfwang na nuna raunin jagoranci da rashin gamsuwar jama’a da ayyukansa a jihar.

APC za ta tarbi sababbin mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta shirya tarbar wasu manyan 'yan siyasa da suka shigo cikinta a jihar Plateau.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar da kwafa wani kwamiti wanda zai kula da tarbar masu sauya shekar.

Kara karanta wannan

Wike ya ragargaji gwamnonin PDP, ya fadi illar da za su yi wa jam'iyyar

Hakazalika ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da kansa zai karɓi manyan ’yan siyasa da suka sauya sheƙa zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng