Shugaban APC Ya Fadi Masu Hannu a Wahalar da ake Sha a Najeriya

Shugaban APC Ya Fadi Masu Hannu a Wahalar da ake Sha a Najeriya

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya shawarci ‘yan Najeriya su riƙa tuhumar gwamnonin jihohi
  • Shugaban ya ce kowanne gwamna yanzu yana karɓar fiye da ninki uku na abin da ake ba su a baya saboda ƙarin kuɗin da aka samu
  • Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana kan hanya madaidaiciya wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina zargi gwamnatin tarayya kawai kan halin ƙuncin da ake ciki.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya shawarci jama'a da su fara riƙe gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi da alhakin duk wata azaba da suke sha.

Kara karanta wannan

Shugabancin PDP: Turaki ya cike fam, ya bar Sule Lamido da barazanar zuwa kotu

Shugaban APC, Nentawe Ylwatda ya zargi gwamnoni da jawo matsaloli a kasa
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda Hoto: Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Yilwatda fadi haka ne yayin taron ƙaddamar da littafi mai suna “Vicious Red Circle”, wanda Alex Oriaku ya rubuta game da safarar mutane.

Shugaban APC ya magantu kan gwamnoni

Nentawe Yilwatda ya ce yanzu ne lokaci mafi dacewa da jama’a za su fara tambayar gwamnoni abin da suke yi da kuɗin da ake rabawa.

Ya bayyana cewa ya kamata jama'a su bincika abin da gwamnonin ke yi ganin yadda aka ƙara yawan abin da suke samu daga gwamnatin tarayya dake Abuja.

Ya ce:

“Babu gwamna a yau da ke karɓar ƙasa da ninki uku na abin da yake karɓa a baya. A da ana raba kusan Naira biliyan 400 a wata, amma yanzu rabon da aka yi na ƙarshe ya kai Naira tiriliyan 2.2."

Shugaban APC na tare da Bola Tinubu

Nentawe Yilwatda, wanda ya karɓi shugabancin lokacin da ake ta suka kan manufofin tattalin arziƙin gwamnati, ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana tafiya bisa hanya mai kyau.

Kara karanta wannan

NDLEA ta gano yadda aka boye miyagun kwayoyi a robobin man shafawa

Shugaban APC ya kare Tinubu daga alhakin wahalhalu a kasa
Shugaban Kasa Bola Tinubu, Nentawe Yilwatda Hoto: Bayo Onanuga/Professor Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ci gaba da jagorantar ƙasar har ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta ke ciki.

An yi maganar safarar mutane

A yayin taron, an kuma tattauna kan batun safarar mutane dake kara kamari a kasar nan ta yadda ake safarar jama'a zuwa sassan duniya.

Darakta-Janar na Hukumar NIA, Mohammed Mohammed, ya bayyana safarar mutane a matsayin ɗaya daga cikin manyan laifuffuka.

Ya ce:

“Safarar mutane ta lalata kyawawan ɗabi’unmu, ta kuma raba mutane mutuncinsu."

Ya ce NIA tana ba da bayanan sirri da tallafi ga Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane (NAPTIP), tare da kiran kungiyoyin farar hula da na addini su shiga cikin wannan yaƙi.

A cikin bayaninsa, marubucin littafin, Alex Oriaku, ya ce manufarsa ita ce bayyana yadda safarar mutane ke cin gajiyar marasa ƙarfi da talakawa.

'Yan APC na neman a takawa matawalle burki

A wani labarin, mun wallafa cewa dattawan reshen Arewa sun bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sa takunkumi kan ayyukan da suka ce Ministan Tsaro Bello Matawalle na yi

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ICAN ta yi hangen nesa, ta gano babbar barazana ga darajar Naira

Sakataren ƙasa na ƙungiyar, Dr. Abbas Sadauki, ya ce an samu rahotanni daga jihohin Zamfara da Kaduna cewa Matawalle na amfani da kudinsa don jawo yan PDP.

Rahotanni daga jihar Zamfara sun nuna cewa sama da mutane 4,000 na PDP sun bar jam’iyyarsu suka koma APC a cikin 'yan makonni da suka gabata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng