2027: Sule Lamido zai Nemi Takarar Shugaban Jam'iyyar PDP na Kasa

2027: Sule Lamido zai Nemi Takarar Shugaban Jam'iyyar PDP na Kasa

  • Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin jam’iyyar PDP a taron da za a yi
  • Sule Lamido ya ce zai ziyarci hedikwatar jam’iyyar PDP a Wadata Plaza domin sayen fom din takara ranar Litinin, 27, Oktoba, 2025
  • Takararsa ta zo ne a daidai lokacin da ake samun rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar kan wanda zai zama zababben dan takarar Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya sanar da kudurinsa na neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP.

Ya ce manufarsa ita ce sake farfado da jam’iyyar PDP da kuma mayar da ita kan turbar da ta shahara da ita a baya, musamman gabanin zabukan 2027.

Kara karanta wannan

Turaki ya kara fuskantar matsala a shirin zama shugaban PDP na kasa

Mai girma Sule Lamido
Sule Lamido, wanda zai nemi takarar shugaban PDP. Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Lamido ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a safiyar Litinin, 27, Oktoba, 2025, inda ya ce zai halarci hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule ya ce zai dawo da darajar PDP

Lamido ya bayyana cewa yana da cikakken imani da tsarin dimokuraɗiyya, tare da jajircewa wajen dawo da martabar PDP a idon ’yan Najeriya.

Ya rubuta cewa:

“Da ikon Allah, yau Litinin, 27, Oktoba, 2025, da karfe 11:00 na safe, zan kasance a Wadata Plaza domin sayen fom din neman kujerar shugaban jam’iyyarmu, PDP.
"Aniyata ita ce in dawo da darajar jam’iyyar.”

Rikicin PDP kan shugabancin jam'iyya

Aniyar takarar Lamido ta biyo bayan rikici da ya taso bayan wasu jiga-jigan Arewa a jam’iyyar sun bayyana tsohon minista Kabiru Tanimu Turaki (SAN) a matsayin dan takara.

Sai dai wasu daga cikin mambobin jam’iyyar, ciki har da magoya bayan Sule Lamido da Nyesom Wike, sun ki amincewa da hakan, suna cewa ba a yi isasshen tuntuba ba kafin yanke shawarar.

Kara karanta wannan

Jiga jigan PDP 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Zamfara, sun fadi dalili

Wannan rikicin ya sake nuna yadda jam’iyyar ke kokarin shawo kan bambance-bambancen da ke cikinta kafin babban taronta na kasa da ake sa ran gudanarwa a watan Nuwamba.

PDP za ta yi taron kasa a jihar Oyo

Rahotanni sun nuna cewa PDP za ta gudanar da babban taronta na kasa mai zabe a Ibadan, Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.

A ranar 25, Oktoba, 2025, jam’iyyar ta fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin tantance ’yan takara na kasa mai mutum 13.

Kwamitin zai yi aiki karkashin jagorancin tsohon dan takarar gwamnan jihar Ondo, Eyitayo Jegede (SAN).

Shugaban PDP na kasa
Shugaban PDP na Najeriya, Damagun. Hoto: People's Democratic Party
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa zai fara aikinsa a ranar Talata, 28, Oktoba, 2025, inda zai tantance duk masu neman mukamai, ciki har da kujerar shugabancin jam’iyyar.

Wike ya ce jam'iyyar PDP ta mutu

A wani labarin, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta riga ta mutu a Najeriya.

Wike ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ya ce hasashen da ya yi kan PDP ya zama gaskiya.

Kara karanta wannan

Bayan murabus daga PDP, ministan Buhari na kokarin 'hana' gwamna shiga APC

Ministan ya kara da cewa yadda mutane ke sauya sheka daga jam'iyyar alama ce da ke tabbatar da maganar da ya yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng