"PDP Ta Mutu Murus": Nyesom Wike Ya Fadi Masu Laifin Kashe Jam'iyyar
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi magana kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP
- Wike ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta dade da mutuwa saboda rashin bin doka da jiga-jigai daga cikinta suka rika yi
- Ministan ya yi nuni da cewa dukkan hasashen da ya yi kan abubuwan da za su faru da jam'iyyar, sai da suka auku
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta dade da mutuwa.
Wike ya bayyana cewa jam’iyyar ta dade da mutuwa saboda rashin bin tsarin dimokuradiyya, girman kai da danniya daga wasu gwamnoninta.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Wike ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Jumma’a, 24 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Wike ya ce kan rikicin PDP?
Ministan ya bayyana cewa bai yi mamaki ba ko kadan kan yadda ake yawan ficewa daga jam'iyyar, inda ya ce dama ya yi gargadin hakan zai faru, rahoton TheCable ya tabbatar da labarin.
"Ina ta fada tun farko, idan abin da ke gudana bai tsaya ba, PDP za ta lalace. Na fada sau da dama cewa idan ba a bi doka ba, za mu yi nadama. To ga abin da yake faruwa yanzu."
“Ba ku ga yadda mutane ke barin jam’iyyunsu ba? Na fada tun farko cewa wannan abin zai zama kamar girgizar kasa. Duk abin da na fada tun farko, babu wanda bai tabbata ba.”
- Nyesom Wike
Wike ya zargi gwamnonin PDP da wasa da makomar jam’iyyar, yana mai cewa irin yadda suke tafiyar da jam’iyyar, zai kai ta ga rugujewa.
"Shin ban fada cewa gwamnoni da dama za su bar jam’iyyar? Gwamnan Enugu shi ne shugaban kwamitin shirya babban taron kasa. Gwamnan Bayelsa kuma shugaban kwamitin rabon mukamai. Amma na san tun farko cewa suna wasa da jam’iyyar."
- Nyesom Wike
Wike ya ce bai ruguza PDP ba
Da aka tambaye shi kan zargin cewa shi ne ya haddasa rugujewar PDP bayan zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na 2022, Wike ya ce abu mai rai ne yake lalacewa ba matacce ba.

Source: Facebook
“Wane gida ku ke cewa na rusa? Gidan da ya mutu tun da dadewa? Idan kun bi doka, za ku samu sakamako mai kyau."
"Na gaya musu tun da farko lokacin da batun sakatare ya taso, ku bi tsarin doka. Amma suka ce su gwamnoni ne. To ga sakamakon yanzu.”
- Nyesom Wike
Abin da Wike zai gayawa Jonathan kan 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan batun takarar Goodluck Jonathan.
Wike ya bayyana cewa zai gayawa tsohon shugaban kasan ra'ayinsa idan ya nemi shawara kan batun fitowa takara a zaben 2027.
Ministan ya ce ba zai ji tsoron komai ba, zai fada wa Jonathan duk abin da ke ransa matukar ya tuntube shi game da fitowa takarar shugaban kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


