Abin da Ya Sa Wasu Gwamnoni da Kusoshin Arewa ke Son Turaki Ya Zama Shugaban PDP

Abin da Ya Sa Wasu Gwamnoni da Kusoshin Arewa ke Son Turaki Ya Zama Shugaban PDP

  • Gwamna Dauda Lawal ya ce sun zabi Kabiru Tanimu Turaki a matsayin wanda suke so ya karbi shugabancin PDP saboda doka ta amince da hakan
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa siyasa ta gaji sabani, don haka ba abin mamaki ba ne don wasu sun nuna ba su yarda daTuraki ba
  • Wannan dai na zuwa ne bayan shugabannin PDP a Arewa ciki har da gwamnoni sun cimma matsaya kan kujerar shugabancin jam'iyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gusau, Zamfara State - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi karin haske kan amincewa da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dan takarar shugaban PDP na masalaha.

Gwamna Lawal ya ce sun marawa tsohon Ministan Harkokin na Musamman, Kabiru Turaki, baya don ya zama shugaban PDP na kasa saboda bai saba wa dokar jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi garambawul a gwamnatinsa, an sauyawa kwamishinoni ma'aikatu

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Hoton gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Dauda Lawal ya ce tanadin kundin tsarin PDP, ya amince da tsarin masahala a matsayin halastacciyar hanyar zaben shugabanni, in ji rahoton Daily Trust

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP a Arewa ta rabu kan zaben Turaki?

A farkon makon nan, manyan jiga-jigan PDP daga Arewa sun gudanar da taron tattaunawa a Abuja, inda suka amince da Turaki a matsayin dan takarar masahala.

Taron ya samu halartar gwamnoni, Bala Mohammed (Bauchi), Caleb Mutfwang (Filato), Ahmadu Fintiri (Adamawa), da Dauda Lawal (Zamfara), tare da mukaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum.

Haka kuma, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon ministan yada labarai Jerry Gana, shugaban sanatocin PDP, Abba Moro, da tsohon ministan ilimi, Ibrahim Shekarau, duk sun halarci taron, in ji The Cable.

Sai dai matakin amincewa da Kabiru Turaki ya jawo rikici a tsakanin wasu jiga-jigan PDP na yankin Arewa maso Yamma, wadanda suka koka cewa ba a gayyace su taron ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya koka kan sabon salon ta'addancin 'yan Boko Haram a Borno

Gwamna Dauda ya fadi dalilinsu na daukar Turaki

Da yake jawabi ranar Juma’a yayin kaddamar kwamitin tantancewa na taron PDP na kasa da ke tafe, Gwamna Lawal ya bayyana cewa sabani irin haka abu ne da ke faruwa a siyasa.

Dauda Lawal ya ce:

“Ko me muka yi, akwai wadanda ba za su ji dadin hakan ba, haka siyasa take. Muna kokarin hada kan kowa cikin jam’iyya domin ci gaban ta.
"Wannan tsari ne da ba za a gama shi lokaci guda ba, amma ina tabbatar muku cewa komai zai yi daidai. Yin sabani al’ada ce a siyasa.”

Gwamnan ya kuma jaddada cewa tsarin amincewa da goyon bayan Turaki ya kasance bisa doka kuma daidai da ka’idodin jam’iyyar.

“A cikin kundin tsarin jam’iyyarmu akwai tanadi kan tsarin masalaha. Don haka babu wani sabon abu a nan. Wannan abu ne na halak, kuma ya dace da dokokin PDP,” in ji shi.
Kabiru Tanimu Turaki.
Hoton tsohon Ministan Ayyuka na Musamma, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Turaki
Source: Facebook

Wani jigin PDP, Rabiu Shitu ya shaida wa Legit Hausa cewa irin wadannan abubuwan ke sa ya fara tunanin da wuya jam'iyyar ta iya shawo kan matsalolinta.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An kama dalibin jami'ar IBB kan saboda gwamna a Facebook

A cewarsa, lokaci ya yi da shugabannin PDP za su ajiye son rai, su sanya kishi da tunanin ceto kasar nan a gaba matukar suna son jam'iyyar ta kai labari.

Rabiu ya ce:

"Ni a ganina bai kamata a samu matsala kan daukar Turaki ba, idan har kana kishin PDP bai kamata ka nuna damuwa kan wannan matakin ba.
"Mu dauka ma Turaki bai cancanta ba, shi kadai zai tafiyar da PDP? Mu fa za mu hada karfi mu mara masa baya, inda ya yi ba daidai ba mu gyara, Allah zai taimake mu.
"Amma abu dan karami sai ka ji wasu sun balle, matukar ba mu gyara ba, bana tunanin za mu kai labari a zabe mai zuwa."

Wike ya nesanta kansa da zaben Turaki

A baya, mun kawo maku rahoton cewa Ministan Harkokin Abuja ya bayyana cewa alamu sun nuna gwamnoni sun kama hanyar kashe jam'iyyar PDP gaba daya.

Wike ya bayyana cewa irin yadda gwamnonin PDP suke tafiyar da rikicin cikin gida na jam’iyyar zai kai ta ga rugujewa.

Tsohon gwamnan ya kuma nesanta kansa daga jiga-jigan jam’iyyar a Arewa da suka amince da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dan takararsu na kujerar shugaban PDP na kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262