Akpabio Ya Kare Sanatocin da Ke Komawa APC, Ya Fadi Abin da Ke Jan Hankalinsu

Akpabio Ya Kare Sanatocin da Ke Komawa APC, Ya Fadi Abin da Ke Jan Hankalinsu

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya tabo batun sauya shekar da 'yan adawa ke yi zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Godswill Akpabio ya bayyana cewa gamsuwa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ne ya sanya ake rububin komawa APC
  • Ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaban kasa Tinubu ke aiwatarwa na ci gaba da samun karbuwa a wajen 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi tsokaci kan sauya shekar da 'yan siyasa na jam'iyyun adawa ke yi zuwa jam'iyyar APC.

Akpabio ya bayyana cewa yawaita sauya shekar zuwa jam'iyyar APC, alama ce ta kishin kasa da kuma tabbacin amincewa da jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Akpabio ya yi magana kan sauya sheka
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Akpabio ya kai sanatoci gaban Tinubu

Jaridar Leadership ta ce Akpabio ya bayyana hakan ne da yammacin Laraba bayan ya jagoranci sababbin ’yan majalisar dattawa biyu domin ganawa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"An samu ci gaba," Sanata Akpabio ya tuna kalaman Marigayi Yar'adua kan zaben Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin da ya jagoranta su ne Sanata Agom Jarigbe (Cross River ta Arewa) da Sanata Kaila Samaila Dahuwa (Bauchi ta Arewa).

Dukkanin sanatocin biyu sun sauya sheka ne daga jam'iyyar PDP zuwa APC. A gefe guda irinsu Mukhtar Dandutse sun soki sauya-shekar.

Akpabio ya ce matakin da ’yan majalisun suka dauka yana nuna yadda goyon bayan jama’a ke karuwa ga sauye-sauyen tattalin arziki da tsare-tsaren cigaban kasa da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa, rahoton jaridar The Cable ya zo da labarin.

“Wadannan sanatoci 'ya'ya ne a wajen shugaban kasa, kuma magoya bayansa ne. Shugaba Tinubu uba ne ga kasa baki daya da kuma dukkan jam’iyyun siyasa."

- Godswill Akpabio

Ya kara da cewa, duk da cewa sanatocin an zabe su ne a karkashin jam’iyyun daban-daban, manufofin shugaban kasa na canza tattalin arziki da kara kudin shiga sun sa suka ga dacewar hadewa da jam’iyya mai mulki.

"Sun shiga majalisar ne ta jam’iyyun siyasa daban-daban, amma saboda irin sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaban kasa ya kawo, sun ga dacewar su hadu don a gina Najeriya."

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin adawa a Najeriya da suka bar jam'iyyunsu zuwa APC a 2025

"Abin da suka yi kishin kasa ne. Ba su damu da wace jam'iyya ke kan mulki ba, amma wanda zai iya inganta rayuwar ’yan kasa."

- Godswill Akpabio

Godswill Akpabio ya kare masu komawa APC
Godswill Akpabio yayin gangamin taron APC Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Sanata ya fadi dalilin komawa APC

A nasa jawabin, Sanata Agom Jarigbe ya bayyana cewa sauyin shekar da ya yi ba siyasa ba ne, sai dai don yana ganin Shugaba Tinubu yana yin abin da ya kamata, wanda hakan ya sa ya yanke shawarar hadewa da shi.

“Na shiga APC ne saboda ina ganin Shugaban Kasa yana kokari sosai. Ina so na shiga na taimaka wajen tabbatar da ganin jama’a sun amfana da dimokuradiyya."

- Agom Jarigbe

'Yan NNPP sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi babban kamu bayan mutane sama da 500 sun sauya sheka daga NNPP zuwa cikinta.

Masu sauya shekar daga jam'iyyar NNPP zuwa APC sun fito daga kananan hukumomin Ungogo da Fagge a jihar Kano.

Wasu daga cikin sababbin mambobin da suka sauya sheka sun bayyana cewa dalilin da ya sa suka koma APC shi ne ganin yadda jam’iyyar ke gudanar da manufofi na cigaban al’umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng