"An Samu Ci Gaba," Sanata Akpabio Ya Tuna Kalaman Marigayi Yar'adua kan Zaben Najeriya
- Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa an samu ci gaba a tsarin gudanar da zaben Najeriya tun bayan kayar da PDP a 2015
- Shugaban Majalisar Dattawan ya fadi haka ne yayin da ake karatu na biyu kan kudirin gyaran dokar zabe ranar Laraba
- Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom dai na daya daga cikin wadanda suka ci zabe a karkashin inuwar jam'iyyar PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa tsarin gudanar da zaɓe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba bayan PDP ta bar mulki.
Sanata Akpabio, wanda ya ci zabe sau da dama a inuwar PDP, ya ce zaben Najeriya ya inganta fiye da lokacin mulkin PDP, wacce ta sha kaye a shekarar 2015.

Source: Facebook
Daily Trust ta tattaro cewa sau biyu Akpabio na samun nasarar lashe zaben gwamnan jihar Akwa Ibom gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, sannan ya ci zaben sanata duk a PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya tuna maganar Umaru Yar'adua
Da yake jawabi yayin da Majalisar Dattawa ke karatu na biyu kan kudirin gyaran dokar zabe, Sanata Akpabio ya ce tsarin zaben Najeriya na kara samun ci gaba tun bayan zaben 2015.
“Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Enyinnaya Abaribe da muka shafe kusan shekaru 25 muna siyasa, mun san cewa jam’iyya ba ta hana mutum nasara.
"Ka na iya lashe zaɓe a kowace jam’iyya idan kana da kwarewa da gogewa. Amma tun bayan da PDP ta bar mulki, tsarin zaɓe a ƙasar nan ya inganta sosai.
"Ina tuna lokacin da na lashe zaɓen gwamna a 2007, marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua, Allah ya ji kansa, ya fito fili ya amince cewa zaɓen da ya kawo shi mulki cike yake da da kura-kurai da maguɗi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana
- Sanata Godswill Akpabio.
"Tsarin zaben Najeriya ya inganta" - Akpabio
Shugaban majalisar dattawan ya kuma amince cewa duk da akwai wasu matsaloli da ake fuskanta har yanzu, tsarin zaben kasar nan ya fi yadda yake a baya.
“Ku duba zaɓen da ya gabata, sai da aka je gaban kotun koli saboda muhawarar ko lashe Abuja (FCT) zai nuna wanda zai zama shugaban ƙasa.
"Wasu suna cewa, idan ka ci Abuja, kai ne shugaban ƙasa, ko da ka sha kaye a jihohi 36. Sun ɓata lokaci suna muhawara a kafafen labarai, amma a ƙarshe kotun koli ta tabbatar da gaskiya.”
“Idan da a ce an yi amfani da tunani, da an san cewa hakan ba manufar dokar zabe ba ce.”

Source: Facebook
Majalisa ta tabbatar da nadin shugaban NPC
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Dr. Aminu Yusuf daga jihar Neja a matsayin sabon shugaban hukumar kidayar jama’a ta kasa (NPC).
Bayan haka, Majalisar ta kuma amince da nadin Joseph Haruna Kigbu da Tonga Betara Bularafa a matsayin kwamishinoni a NPC.
Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar kan shaidar dan kasa da kidaya, wanda Sanata Victor Umeh, dan majalisar Anambra ta Tsakiya, ya jagoranta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

