Gwamnonin PDP a Arewa Sun Cin Ma Matsayar Wanda Suke So Ya Shugabanci Jam'iyyar

Gwamnonin PDP a Arewa Sun Cin Ma Matsayar Wanda Suke So Ya Shugabanci Jam'iyyar

  • Shugabannin PDP ciki har da gwamnoni daga yankin Arewa sun tsayar da dan takarar da suke so ya shugabanci jam'iyyar
  • Sun dai cin ma wannan matsaya ne a wani babban taron da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba
  • Shugabannin sun amince da tsohon ministan harkoki na musamman, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin dan takarar da suke goyon baya

Editan ​Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugabannin PDP daga Arewa, ciki har da gwamnoni, sun cin ma matsaya kan dan takarar da suke son ya shugabanci jam'iyyar.

Shugabannin sun amince da tsohon ministan harkoki na musamman, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin dan takararsu don kujerar shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar da ke tafe a watan Nuwamba.

Gwamnonin PDP na son Tanimu Turaki ya zama shugaban jam'iyyar
Babban jigo a jam'iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Tanimu Turaki
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ne ya bayyana haka bayan taron shugabannin PDP na Arewa da aka gudanar da yammacin ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gana da Shugaba Tinubu bayan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su waye mahalarta taron na PDP?

The Cable ta ce mahalarta taron sun hada da Gwamna Bala Mohammed (Bauchi), Gwamna Caleb Mutfwang (Plateau) da Gwamna Ahmadu Fintiri (Adamawa).

A taron kuma akwai Gwamna Dauda Lawal (Zamfara), tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Sauran sun hada da tsofaffin gwamnoni Ahmed Makarfi (Kaduna), Ibrahim Shekarau (Kano), Farfesa Jerry Gana da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) daga Arewa karkashin jagorancin mukaddashin shugaban jam’iyyar, Ambasada Umar Damagum.

An amince Tanimu Turaki ya shugabanci PDP

“Mun amince da Tanimu Turaki a matsayin dan takararmu, amma hakan ba yana nufin hana kowa tsayawa takara ba. Kundin tsarin jam’iyyar ya bai wa kowane mamba ’yancin gwada karbuwarsa a zaben da za a gudanar a babban taron kasa."

- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa amincewa da Turaki na nufin tabbatar da zaman lafiya da nasarar taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta kori mataimakin shugaba da wasu manyan jami'ai 8, an fadi dalili

“Manufar wannan amincewa ita ce tabbatar da daidaito da hadin kai kafin babban taron. Sauran mukamai kuma za a tattauna su ne a matakin yankuna."

- Ahmadu Umaru Fintiri

Gwamnonin PDP sun zabi dan takara
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri Hoto: @GovernorAUF
Source: Original

Ana kokarin hana babban taron PDP

Duk da cewa kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar Oktoba 31 domin yanke hukunci kan shari’ar da ke neman hana gudanar da taron, jam’iyyar ta ci gaba da shirye-shiryenta.

Wadanda suka shigar da karar, Austine Nwachukwu (shugaban PDP na Jihar Imo), Amah Abraham Nnanna (shugaban PDP na Abia), da Turnah George (sakataren PDP na Kudu maso Kudu), sun shigar da kara suna neman a hana babban taron.

Masu shigar da karar wadanda magoya bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ne, sun kalubalanci sahihancin shirya taron, tare da neman umarnin kotu da ya hana jam’iyyar ci gaba da shirin gudanar da shi.

Dattawan PDP sun kalubalanci Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar dattawan PDP a Arewa ta yi zarge-zarge kan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Kungiyar dattawan na PDP ta zargi Wike da yunkurin ruguza jam'iyyar tare da sauran jam'iyyun adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

LP ta gano hanyar da Peter Obi zai iya kifar da Tinubu cikin sauki a 2027

Sai dai, ta bayyana cewa ministan da 'yan kanzaginsa da ke PDP ba za su yi nasara ba kan yunkurin da suke yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng