Kwankwaso Ya Tura Sako ga Masu Barin Kwankwasiyya, Ya Ce za su Gane Kurensu a 2027
- Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya gargadi masu barin tafiyar NNPP da Kwankwasiyya
- Sanata Kwankwaso ya yi gargadi cewa duk wanda ya yi sakaci da tafiyar Kwankwasiyya, zai gane kuskurensa gaba
- Tsohon gwamnan Kano ya yi hasashen cewa zaɓen 2027 ba zai zama irin na baya ba, musamman ta fuskar magudi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi gargaɗi ga mutanen da ke barin jam’iyyar NNPP ko tafiyar Kwankwasiyya.
Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano ne ya yi gargadin cewa masu yi wa Kwankwasiyya tawaye sun sayi igiyar zarge wuyansu a zaɓen 2027.

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa cewa Kwankwaso bayyana hakan ne yayin da yake ci gaba da shagulgulan cikarsa shekara 69 da haihuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso: Kwankwasiyya na nan daram
Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso ya jaddada cewa siyasarsa ba za ta samu tasgaro ba duk da ficewa da wasu ke yi daga tsarin Kwankwasiyya.
Ya ce:
“A wannan zamani, idan wani yana tunanin zai iya barin tafiya ya koma gefe, ya zo Kano ya ce zai ciri kujera, to idan akwai wanda kansa ya ɗaure to wannan ne. Tafiyarmu za ta ci gaba da hukunta irin waɗannan.".
Hashen Kwankwaso kan za su 2027
Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne ya ce tafiyarsu ba ta da niyyar yin adawa da kowa, sai dai su kan ɗauki mataki idan wani ya nuna raini ko ya ci zarafinsu.
Ya ce:
“Mu ba mu son ɓata da kowa. Amma idan ka wulaƙanta mu, kana zazzare idanu a talabijin da rediyo kana nuna kai wani ne, bayan mun san tarihinka, to za mu ɗauki mataki."

Source: Facebook
Da aka tambaye shi game da yiwuwar maguɗin zaɓe a 2027, Kwankwaso ya bayyana cewa wannan karon zaɓen ba zai kasance kamar na baya ba.
A kalamansa:
“Wasu suna hayaniya suna cewa za su kayar da mu. Amma ni na sani, zaɓen da za a yi a 2027 ba irin na baya ba ne. Matasa yanzu sun farka, kowa gaskiya yake nema. Ba wanda zai sake zuwa ranar zaɓe ya ce za a ba shi kuɗi ya yi zaɓe."
Kwankwaso ya kuma ƙara da cewa matasa suna da muhimmiyar rawa a babban zaɓe da ke ƙaratowa.
Ya kuma bayyana cewa idan aka yi zaɓen gaskiya da rikon amana da adalci, tafiyarsu ce za ta fi samun nasara a kan sauran jam'iyyun siyasa.
Abba ya yi magana kan alaƙarsa da Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce babu wani “dan hassada” daga ciki ko wajen jam’iyya da zai iya shiga tsakanin sa da Rabi'u Musa Kwankwaso.
Gwamna Abba ya yi wannan zazzafan martani ne a lokacin bikin cika shekaru 69 da haihuwar tsohon Sanata, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da aka gudanar a jihar Kano.
Haka kuma ya ce dangantakarsu da Sanata Kwankwaso za ta ci gaba da ƙarfafa, duk da yunkurin wasu da ke son ganin an samu sabani tsakaninsu ko yada cewa sun baɓe.

Kara karanta wannan
"Allah zai tona asirinsu": Tsohon sakataren gwamnatin Kano ya budewa Kwankwaso wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


