Jam'iyyar ADC Ta Kori Mataimakin Shugaba da Wasu Manyan Jami'ai 8, an Fadi Dalili

Jam'iyyar ADC Ta Kori Mataimakin Shugaba da Wasu Manyan Jami'ai 8, an Fadi Dalili

  • Jam'iyyar ADC ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu daga cikin shugabanninta a jihar Kaduna bayan ta zarge su da yin wasu laifuffuka
  • Kwamitin zartarwa na APC ya kori mataimakin shugaba tare da wasu manyan jami'ai guda takwas
  • Korar na zuwa ne bayan an zarge su da aikata abubuwan da suka saba da kundin tsarin mulkin jam'iyyar

Editan ​Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kwamitin zartarwa na ADC a Kaduna ya kori mataimakin shugaban jam’iyyar na jihar, Ahmed Tijani Mustapha.

ADC ta kori mataimakin shugaban ne tare da wasu manyan jami'ai takwas saboda zargin aikata manyan laifuffuka na kin bin doka da cin amanar jam’iyya.

ADC ta kori mataimakin shugaba a Kaduna
Shugaban jam'iyyar ADC na kasa, David Mark Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce hukuncin korar ya fito ne daga cikin matsayar da kwamitin ya cimma a taron da ya gudanar a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa jam'iyyar ADC ta yi korar?

Kara karanta wannan

Dattawan PDP sun nuna yatsa ga Wike kan rikicin jam'iyyar

A yayin taron an tabbatar da cewa wadanda aka kora sun aikata laifuffukan da suka hada da rashin biyayya ga shugabanci, shirya tarurrukan sirri domin kifar da shugabanci.

Sauran laifuffukan sun hada da amfani da takardun bogi, karbar kudi daga mambobi ba bisa doka ba.

Sauran wadanda aka kora sun hada da sakataren yada labarai, Idris Musa, mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyya ta daya, Sulaiman Abdullahi da ma'aji na jiha Gambo Sani.

Hakazalika cikin wadanda aka kora akwai sakataren kudi, Magaji Maiwada, lauyan jam'iyya, Danlami Dabai Musa, mai kula da nakasassu, Saura Muhammed da mataimakin shugaban matasa, Ibrahim Muhammed.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Elder Patrick Ambut, ya bayyana cewa shugabancin ADC a Kaduna ya kudiri aniyar kare zaman lafiya, biyayya da bin doka kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada, rahoton The Punch ya zo da labarin.

“Abin da mataimakin shugaban jam’iyyar ya yi babbar barna ce da ta sabawa doka. Ayyukansa sun janyo rashin jituwa a cikin jam’iyya a jiha da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya."

- Elder Patrick Ambut

ADC na son kare kundin tsarin mulki

Kara karanta wannan

Kotu ta fadi dalilin dage zaman shari'ar kwamandojin 'Yan ta'addan Ansaru

Ya ce manufar jam’iyyar ita ce kare kundin tsarin ADC da tabbatar da cewa ya ci gaba da kasancewa cikin gaskiya da doka.

ADC ta kori wasu shugabanninta a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
“A matsayinsa na mataimaki, bai da ikon gudanar da taro ko bayar da umarni ba tare da bin matakai na doka ba. Wannan ya saba wa tsarin jam’iyyar kuma muna tabbatar da cewa ba za mu lamunta da hakan ba."

- Elder Patrick Ambut

Elder Patrick Ambut ya jaddada cewa ADC a Kaduna za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin lumana da mutunta tsarin jam’iyya domin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a tsakanin mambobi.

ADC ta yi magana kan tsare Nnamdi Kanu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi tsokaci kan tsare jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa ba ta cimma wata matsaya kan tsare shi ba domin lamarin yana gaban kotu.

Ta bayyana cewa ba daidai ba ne ta yi magana kan shari'arsa wadda ake yi sakamakon tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya take yi masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng