PDP Ta Sake Shiga Tsilla Tsilla bayan 'Dan Majalisa Ya Sauya Sheka zuwa APC
- 'Yan siyasa na ci gaba da sauya sheka daga jam'iyyun adawa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Jam'iyyar PDP ta rasa dan majalisar wakilai daya tilo da take da shi a jihar Benue bayan ya sauya sheka zuwa APC
- Dan majalisar ya bayyana cewa ya tattara 'yan komatsansa daga PDP ne saboda rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Apa/Agatu ta jihar Benue, Hon. Ojema Ojotu, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Hon. Ojema Ojotu ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai adawa zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Hon. Ojema Ojotu ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC ne a hukumance yayin zaman majalisar na ranar Talata, 21 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan majalisun APC sun karu a Benue
Kafin yanzu, jam'iyyar APC ta samar da kujeru 10 cikin 11 na majalisar wakilai da ake da su a jihar Benue.
Sauya shekarsa ta sanya yanzu dukkanin kujerun 'yan majalisar wakilai daga jihar Benue na hannun jam'iyyar APC.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Talata, ne ya sanar da sauyin shekar Ojotu bayan karanta wasikar da dan majalisar ya aiko.
Meyasa dan majalisar PDP ya koma APC?
A cikin wasikar, Ojema Ojotu ya bayyana cewa shawarar barin PDP ta biyo bayan rikice-rikicen da suka dade suna addabar jam’iyyar ba tare da samun mafita ba.
“Bayan tuntubar mutanen mazabata, iyalaina da abokanan siyasa, na yanke shawarar barin jam’iyyar PDP domin shiga APC."
- Hon. Ojema Ojotu
An samu turjiya kan sauya shekar
Sai dai sauya shekar ya fuskanci kalubale daga bangaren ’yan adawa, inda mataimakin shugaban marasa rinjiye na Majalisar, Hon. Aliyu Madaki na jam’iyyar NNPP, ya bukaci a ayyana kujerar Ojotu a matsayin fanko.

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
“Mai girma shugaban majalisa, ina dogaro da tanadin kundin tsarin mulki sashe na 68(1)(g) wanda ya bayyana cewa idan dan majalisa ya bar jam’iyyar da ta dauki nauyinsa, kuma babu rarrabuwar kai a cikinta, dole a soke kujerarsa."
- Hon. Aliyu Madaki
Sai dai, shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Ibrahim Halims, ya kare matakin da Ojema Ojotu ya dauka na ficewa daga jam'iyyar PDP, rahoton Daily Post ya tabbatar da.labarin.
“Idan jam’iyya ta kasa warware rikicinta, kuma babu zaman lafiya a cikinta, dan majalisa yana da hakkin barinta domin kare makomarsa ta siyasa.”
- Ibrahim Halims

Source: Facebook
An yi wa Ojotu maraba zuwa APC
A jawabinsa, mataimakin shugaban majalisar, Hon. Benjamin Kalu, ya taya Ojema Ojotu murnar shiga APC, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan jam’iyyar da ’yan majalisar daga yanzu.
Hon. Ojema Ojotu shi ne shugaban kwamitin majalisar kan hanyoyin ruwa na cikin gida.
Dalilin gwamnoni na komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya fadi dalilin da ya sa gwamnoni ke sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa gwamnonin na jam'iyyun adawa suna komawa APC ne saboda manufofin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu take aiwatarwa.
Ya nuna cewa gwamnonin ba suna komawa APC ba ne don ganin sun lashe zabe a zaben shekarar 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

