LP Ta Gano Hanyar da Peter Obi Zai Iya Kifar da Tinubu cikin Sauki a 2027

LP Ta Gano Hanyar da Peter Obi Zai Iya Kifar da Tinubu cikin Sauki a 2027

  • 'Yan siyasa na ci gaba da batun zaben shugaban kasan Najeriya na shekarar 2027 da ake tunkara
  • Jam'iyyar LP ta sake jaddada matsayarta kan kiran 'yan adawa da su zama tsintsiya madaurinki daya wajen fuskantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Ta bayyana cewa akwai abin da Atiku Abubakar zai iya yi wanda zai sanya a kifar da Mai girma Tinubu a lokacin zabe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar LP ta sake tayar da muhawara kan bukatar hadin kan jam’iyyun adawa don kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Bangaren jam’iyyar da ke goyon bayan Peter Obi da gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa hadin kai ne kadai zai iya kifar da Shugaba Tinubu.

LP ta ba Atiku shawara kan kifar da Tinubu a 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi Hoto: @atiku, @PeterObi, @DOlusegun
Source: Twitter

Mai rikon mukamin sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar LP, Prince Tony Akeni, ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya ba Shugaba Tinubu shawara kan yajin aikin ASUU

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace bukata LP ta nema wajen Atiku?

Prince Tony Akeni ya roki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya ajiye burinsa na sake neman takarar shugabancin kasa.

Ya bukaci Atiku ya marawa Peter Obi baya idan da gaske yana son ceto Najeriya daga azabar rashin nagartaccen shugabanci.

"Idan Atiku zai duba zuciyarsa da gaskiya kuma ya nuna cewa yana son kasar nan da gaske, ya goyi bayan Peter Obi a matsayin shugaban kasa, zai iya zabar duk wanda ya ke so, ko dan autansa ne a matsayin mataimaki."
"Tinubu zai zama shugaban kasan da ke kan mulki da za a iya kayar da shi cikin sauki a 2027, amma hakan zai gagara ne kawai idan Atiku ya nace sai ya tsaya takara ta kowane hali."

- Prince Tony Akeni

Prince Tony Akeni ya bayyana hadin kan ’yan adawa a matsayin maganin da zai kawar da annobar son mulki da ke ba jam’iyya mai mulki damar cin nasara a kai a kai.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan APC sun ja kunnen shugaban jam'iyyar kan tazarcen Tinubu a 2027

Jam'iyyar LP ta caccaki Tinubu

Ya kuma caccaki gwamnatin Tinubu da cewa ta maida hankali wajen karbar ’yan gudun hijirar siyasa, yana mai gargadin cewa jam’iyyar APC na dab da rushewa.

LP na son Atiku ya goyi bayan Peter Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi. Hoto: @PeterObi
Source: Facebook
"Bana jin tsoron tsarin jam’iyya daya. Abin da ya kamata a fadawa Tinubu da abokansa shi ne tausayawa. Mu a LP muna tausaya masa saboda yadda yake tattaro ’yan canza sheka."
“Lokacin da abin ya tarwatse, kada ya manta mun yi masa kashedi tun da wuri. Abin da yake yi yanzu shi ne lodawa jirginsa kaya masu nauyi, alhali yunwa da talauci na tarwatsa kasar nan."

- Prince Tony Akeni

Peter Obi ya magantu kan takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya bada tabbacin zai sake fitowa takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Peter Obi ya kuma ba 'yan Najeriya tabbacin cewa zai canza kasar nan ta fuska mai kyau cikin shekaru hudu kacal idan aka damka masa ragamar kasar nan a 2027.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a jam'iyyar hadaka, an dakatar da mataimakin shugaban ADC na kasa

Tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya nuna cewa ko kadan 'yan Najeriya ba za su yi nadamar zabensa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng