Bayan Gwamnoni 2 Sun Fita, Gwamnan PDP Ya Kawo Karshen Jita Jitar Zai Koma APC
- Ana rade-radin cewa Gwamna Ademola Adeleke zai bi sahun gwamnonin jihohin Enugu da Baylesa wajen ficewa daga PDP
- Gwamma Adeleke ya musanta duka rahotanni da ake jingina masa cewa yana shirin barin PDP tare da komawa APC mai mulkin kasa
- Ya ce rikicin da ke faruwa a PDP zai zama tarihi domin sun fara tattaunawa domin warware duk wani sabani a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya ce babu wani shirin da yake yi na komawa jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan.
Gwamnan yana nan daram a jam'iyyar PDP, inda ya jaddada cewa suna ci gaba da zaman tattaunawa domin zakulo duk wasu matsaloli tare da magance su.

Source: Twitter
Ademola Adeleke ya fadi haka ne yayin hira da yan jarida bayan taron farko da kwamitin shirya gangamin PDP ya gudanar a Abuja, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP na kokarin shawo kan rikicinta
Gwamnan Osun ya bayyana rikicin da ake gani a jam’iyyar PDP a matsayin lamarin cikin gida na ’yan uwa da za a warware shi nan ba da jimawa ba.
A cewarsa:
“Muna ci gaba da tarurruka, muna tattauna matsalolinmu na cikin gida. Wannan lamari ne na iyali, ba ma so wani daga waje ya ƙara masa suga, barkono ko gishiri. PDP gida ɗaya ce, kuma mun san yadda za mu tafiyar da al’amuranmu.
“Mun kammala taron farko na kwamitin tsara masaukin baki. Kowa ya halarta, kuma mun warware duk matsalolin da suka taso domin babban taron mu ya gudana lafiya.”
Gwamna Adeleke ya tabo masu sauya sheka
Wannan kalamai na Adeleke na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan Enugu, Peter Mbah ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yayin da Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya fita daga jam'iyyar.
Da yake tsokaci kan masu sauya sheƙa, Gwamna Adeleke ya ce ba su damu ba domin kowane ɗan siyasa yana da ’yancin yanke shawarar da yake so, amma hakan ba zai shafi karfin jam’iyyar PDP ba.
"Har yanzu PDP tana da mambobi masu ƙarfi da goyon baya a faɗin Najeriya. Don haka damu da masu fita daga cikinta ba,” in ji shi.

Source: Instagram
Gwamnan Osun na shirin komawa APC?
Ya kuma musanta jita-jitar da ke cewa yana shirin komawa APC saboda yana da abokai a cikin jam’iyyar.
A rahoton Daily Post, Adeleke ya kara da cewa:
“Ni mutum ne mai wayewa. Idan abokaina da ke cikin APC suka gayyace ni zuwa bikin aure ko wani taron zamantakewa, zan halarta. Amma hakan ba yana nufin na koma APC ba.
"Yanzu haka, ni ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Shirya Babban Taron PDP da za a gudanar a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, kuma har yanzu ina da alaka mai kyau da PDP.”
Gwamna Adeleke zai koma jam'iyyar ADC?
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya musanta jita-jitar cewa zai sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ADC.
Gwamna Adeleke ya nesanta kansa daga batun komawa ADC, inda ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP.
Mai magana da yawun gwamnan Osun, Olawale Rasheed ya bayyana cewa rahoton sauya shekar karya ce da wasu ke yadawa domin tayar da rudani a zukatan jama’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


