Rigima Ta Danno Kai a Jam'iyyar Hadaka, An Dakatar da Mataimakin Shugaban ADC na Kasa

Rigima Ta Danno Kai a Jam'iyyar Hadaka, An Dakatar da Mataimakin Shugaban ADC na Kasa

  • Rikici na neman sake barkewa a jam'iyyar hadakar yan adawa watau ADC yayin da ake ta shirye-shiryen zaben 2027
  • ADC reshen jihar Kuros Riba ta dakatar da Mataimakin Shugaban Jam'iyyar na Kasa (Kudu maso Kudu), Dr. Usani Usani
  • Ta kuma yi fatali da nadin Jackie Wayas a matsayin mataimakiyar kakakin ADC na kasa, ta bukaci uwar jam'iyyar ta sake nazari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - ADC ta dakatar da Mataimakin Shugabanta na kasa (Kudu maso Kudu), Dr. Usani Usani, bisa abin da ta bayyana da yunkurin ruguza hadin kai da ci gaban jam'iyyar.

Kara karanta wannan

A kai kasuwa: APC ta yi watsi da 'yunkurin sauya shekar' gwamnan Filato

Dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take, ta biyo bayan taron kwamitin gudanarwa na jihar Kuros Riba (SWC) da aka gudanar a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025.

Jam'iyyar ADC.
Hoton tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @ADCngCoalation
Source: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa Mai Magana da Yawun Jam’iyyar ADC na Kuros Riba, James Otudor, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa ADC ta dakatar da Usani?

Ya bayyana cewa kwamitin ya gano cewa halayen Dr. Usani na baya-bayan nan sun sabawa kundin tsarin jam’iyyar da kuma ka’idojin da aka gina ta a kai, in ji rahoton TVC News.

Otudor ya ce kwamitin ya duba wasu korafe-korafe da dama da ke zargin Dr. Usani da cin amanar ADC, rashin biyayya ga shugabanci, da aikata abubuwan da ka iya lalata suna da damar jam’iyyar a zaɓe.

“A bisa tanadin kundin tsarin jam’iyya da dokokin ladabtarwa, dakatarwar Dr. Usani za ta ci gaba da aiki har sai an kammala bincike," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun hallaka kwamandan bataliyar sojojin Najeriya da wasu jami'ai

ADC ta soki nadin Jackie Wayas

Bugu da kari, James Otudor ya yi fatali da nadin Jackie Wayas a matsayin mataimakiyar kakakin ADC na kasa, inda ya ce ba a tuntubi shugabannin jam'iyya na Kuros Riba ba.

Otudor ya zargi Wayas da rashin hulɗa da shugabanni na jihar tun bayan nadinta, tare da nuna shakku kan gaskiyarta wajen kare haɗin kan jam’iyyar ADC a yankin Kudu maso Kudu.

“Saboda haka, muna rokon uwar jam'iyya ta sake duba nadinta tare da maye gurbinta da mutum mai ƙwarewa, gaskiya da jajircewa daga Jihar Kuros Riba wanda ke yiwa ADC hidima,” in ji sanarwar.
Shugaban ADC na kasa, David Mark.
Hoton mukaddashin shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark da tambarin jam'iyyar Hoto: @DavidMark
Source: Twitter

Har ila yau, ADC reshen Kuros Riba ta nuna damuwa da wasu daga cikin mambobin kungiyar Coalition Movement ba, wadanda duk da cewa sun shiga jam’iyyar, sun kasa kammala rajistar mambobinsu ba.

Jam’iyyar ta gargade su cewa ba za ta lamunci mambobin da ke cikin jam’iyyu biyu ba ko kuma waɗanda ke amfani da ADC wajen biyan muradunsu na siyasa.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi hanya 1 da APC za ta iya lashe zaben gwamna a jihar Oyo

ADC ta maida martani ga APC

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana cewa sauya shekar gwamnoni da manyan yan siyasa ba zai hana APC shan kaye ba a zaben 2027.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi ikirarin cewa akwai wasu jagororin ADC da za su koma jam'iyya mai mulki nan kusa.

Mai magana da yawun ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ya ce duk wannan shure-shuren da APC ke yi ba za su hana ta mutuwa ba a zabe mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262