Sauya Sheka: Jam'iyyar ADC Ta Taso APC Mai Mulki a Gaba

Sauya Sheka: Jam'iyyar ADC Ta Taso APC Mai Mulki a Gaba

  • Jam'iyyar ADC ta tanka bayan shugaban APC na kasa ya bayyana cewa daga cikin jiga-jiganta za su koma jam'iyya mai mulki
  • Mai magana da yawun ADC na kasa ya bayyana cewa APC ta fuskanci cewa 'yan Najeriya sun koma tsanarta
  • Bolaji Abdullahi ya nuna cewa sauya shekar da ake yi zuwa APC, ba zai hana ta faduwa ba a babban zaben shekarar 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi magana kan sauya shekar da wasu 'yan siyasa ke yi zuwa APC mai mulki.

ADC ta bayyana cewa sauya shekar da ake ta yi ba za ta iya ceto jam’iyyar mai mulki daga faduwa a zaben shekarar 2027 ba.

Jam'iyyar ADC ta caccaki APC
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta kare ba: Gwamna na iya rasa kujerarsa bayan barin PDP da ta kawo shi

ADC ta yi wa jam'iyyar APC martani

Kalaman nasa martani ne ga maganar da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya yi inda ya bayyana cewa wasu fitattun mutane daga ADC za su koma APC nan bada dadewa ba.

Bolaji Abdullahi ya ce gaggawar da ake yi wajen shiga APC daga jam’iyyu daban-daban na nuna cewa jam’iyyar mai mulki ta gane cewa ta zama mara farin jini a idon talakawa, waɗanda suke cikin kunci da wahalar tattalin arziki da gwamnatin APC ta jefa su.

“Gaskiyar magana ita ce APC ta fahimci cewa ta zama jam’iyyar da aka fi tsana a Najeriya, kuma babu adadin sauya shekar da zai iya ceton ta daga fushin ‘yan Najeriya da gwamnatinta ta lalata rayuwarsu tun bayan hawa mulki."

- Bolaji Abdullahi

Ya kara da cewa sauya shekar da ake gani yanzu makarkashiyar shugabanni ne da ke neman kare kansu daga fushin jama’a, ba don amfanin talakawa ba.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin APC ta jawo yunwa da matsalar tsaro a Najeriya, ADC ta fasa kwai

“Mun bayyana a baya cewa waɗannan sauya shekar na manyan mutane da ake gani wata manufa ce ta shugabanni da suka bar jama’a cikin talauci, suna neman ceto kansu ne kawai."

- Bolaji Abdullahi

Bolaji Abdullahi ya kuma ce abin dariya ne yadda APC ke ikirarin cewa wasu fitattun mambobin ADC za su koma gare ta, amma bata iya bayyana sunayensu ba.

“Mun yi mamaki ko APC ta rasa gwamnonin da za ta iya yaudara, yanzu ta koma yin maganar wasu boyayyun mutane daga ADC? Idan har waɗannan mutanen da suke magana akai suna da muhimmanci, to a bayyana sunayensu."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta yi wa APC martani kan sauya sheka
Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

ADC ta kwatanta APC da PDP

Ya ce abin da APC ke yi yanzu daidai yake da abin da jam’iyyar PDP ta yi a lokacin da take da karfi, wanda daga baya ya jawo mata faduwa.

"Babu sabon abu a wasan da APC ke yi yanzu. Shi ne dai irin wasan da PDP ta yi a lokacin da take da iko."

- Bolaji Abdullahi

A karshe, kakakin na ADC ya jaddada cewa APC za ta koyi darasin cewa asalin mulki na dimokuraɗiyya yana hannun jama’a ne, ba na ‘yan siyasar da ke neman iko ba.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan bullo da wani shirin kifar da Tinubu a 2027

An dakatar da shugaban APC a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta dauki matakin ladabtarwa kan daya daga cikin shugabanninta a jihar Edo.

Jam'iyyar ta dakatar da shugabanta na mazaba ta 9 a karamar hukumar Etsan ta Gabas bisa wasu zarge-zarge da take yi masa.

Ta umarci a hana shi halartar dukkanin wasu abubuwan da suka danganci jam'iyyar har zuwa lokacin da za a dage dakatarwar da aka yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng