Ministan Tinubu Ya Fadi Hanya 1 da APC Za Ta iya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Oyo

Ministan Tinubu Ya Fadi Hanya 1 da APC Za Ta iya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Oyo

  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya nemi ‘yan APC su hakura da duk sabani su hada kai don kayar da PDP a 2027
  • Adelabu, wanda ke neman takarar gwamnan Oyo a 2027, ya tabbatar da cewa zai aiwatar da aikin wuta, tituna a mulkinsa
  • Ya ce goyon bayan TAMPAN da OAPs zai taimaka wajen fadakar da jama’a alfanun zabarsa matsayin gwamnan Oyo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo – Mai neman takarar gwamna a 2027 karkashin APC, Chief Adebayo Adelabu, ya bukaci mambobin jam’iyyar su ajiye duk wani bambanci, su hada kai don karfafa matsayinta a Oyo.

Adelabu, wanda shi ne ministan makamashi na Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron shugabanni da mambobin jam’iyyar a yankin Ibarapa.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce sai an samu hadin kai a APC za a iya kwatar Oyo daga PDP.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya halarci wani muhimmin taro a Katsina. Hoto: @BayoAdelabu
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto Adelabu ya ce:

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi karin haske kan bukatar dawo da zaben 2027 zuwa 2026

“Babu wata jam’iyya da za ta iya fafatawa da APC idan muka kasance tsintsiya madaurinki daya. Lokaci ya yi da za mu yafi juna, mun manta da duk sabanin da aka samu a baya."

Ya kara da cewa jihar Oyo ce ke da asalin mutanen da ke da tunanin ci gaba tun lokacin da jam’iyyun farko suka kafa ta.

“Oyo jiha ce ta masu hangen nesa, dole mu dawo da ita zuwa tafarkin ci gaba a 2027,” in ji minista Adelabu.

Minista ya yi alkawarin yin ayyuka a Osun

Ministan makamashi ya bayyana cewa gwamnati ta ware kudade don kammala tashoshin wuta uku a yankin Ibarapa, wadanda aikinsu ya tsaya shekaru da dama ba tare da an kammala su ba.

“Aikin zai fara nan da mako guda. Wannan alkawari ne, ba siyasa ba. Kafin karshen wa’adina, za ku ga haske a dukkan sassan Ibarapa,” in ji Adelabu.

Ya ce an kuma fara rarraba fitilun tituna masu amfani da hasken rana domin tabbatar da tsaro da saukaka harkokin kasuwanci a yankin.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

Adelabu zai farfado da tattalin arziki

Adelabu ya ce matsalolin hanyoyi da tattalin arzikin yankin za su zama tarihi idan aka ba shi amanar mulkin jihar.

“Ba za mu iya samun ci gaba ba idan hanyoyi sun lalace. Gyaran su na cikin ajandar farko ta gwamnati na,” in ji Adelabu.

Ya bukaci jama’a su ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugabancin Tinubu na tafiya kan hanya madaidaiciya.

“Tinubu yana son kasar nan, bai taba son wani dan kasa ya wahala ba."

- Chief Adebayo Adelabu.

Adebayo Adelabu ya ce zai gyara wuta, tituna da farfado da tattalin arziki idan ya zama gwamnan Oyo
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu yana magana da 'yan jarida a Abuja. Hoto: @BayoAdelabu
Source: Twitter

inista ya nemi hadin kan TAMPAN da OAPs

A wani bangare na kokarinsa na fadada turbar siyasa, Adelabu ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar TAMPAN da On Air Personalities (OAPs) a gidansa da ke Iyaganku, Ibadan, inji rahoton Punch.

Ya ce:

“Ku ne muryar jama’a, ku ne ke tsara tunanin al’umma. Ina bukatar goyon bayanku don mu gina Oyo tare, mu samar da cigaba.”

Kara karanta wannan

'Ku rubuta wasiyya ga iyalanku': Gwamna ga masu neman raba shi da mulkinsa

A cewarsa, hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu nishadi zai taimaka wajen inganta wayar da kan jama’a da kuma karfafa kishin kasa.

Adelabu zai nemi takarar gwamnan Oyo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya fito fili ya jaddada kudirinsa na shiga tseren takarar gwamnan Oyo a 2027.

Mista Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ya bi matakai da dama na neman gwamnan tun 2019 kuma lokaci ya yi da zai mulki Oyo.

Ministan makamashin ya yi amfani da kalmar “Emi lokan” wadda ke nufin “Lokaci na ne” da Bola Tinubu ya yi amfani da ita a lokacin yakin zabensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com