'Ku Shirya': Malami Ya Jero Gwamnoni 7 da Ka Iya Faduwa a 2027, Ya Gargadi Akpabio
- Limamin cocin INRI, Fasto Elijah Ayodele, ya sake yin hasashen abin da zai faru da wasu gwamnoni a Najeriya
- Malamin ya gargadi gwamnoni bakwai na Najeriya cewa samun wa’adin biyu a 2027 babu tabbaci
- Ayodele ya kuma ja kunnen Akpabio da Ned Nwoko, yana cewa suna iya rasa kujerunsu a zaben mai zuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Limamin cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya kuma yin hasashe game da zaben 2027.
Malamin addinin Kirista ya gargadi gwamnoni bakwai na Najeriya cewa samun wa’adin biyu a 2027 babu tabbaci.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa Osho Oluwatosin ya sanya hannu wanda jaridar Tribune ta gano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen Fastokan ficewar gwamnonin PDP
Ayodele ya sha yin hasashe game da siyasar Najeriya inda ya tabo batun wasu gwamnoni guda hudu da ya ce za su iya shiga APC.
Babban malamin addinin Kirista, Ayodele ya yi hasashe mai ban mamaki game da wasu gwamnonin adawa da za su iya komawa APC.
Malamin ya gargadi ga Bola Tinubu cewa wasu gwamnonin adawa za su koma APC amma ba duka ne ke son taimaka masa.
Limamin ya ce wasu daga cikinsu za su shiga jam’iyyar ne kawai don su sami albarkar shugaban ƙasa da kuma neman mukamai.

Source: Facebook
Gwamnonin da za su iya rasa kujerarsu
A cikin sanarwar, Ayodele ya bayyana cewa gwamnoni daga Kudancin Najeriya kamar Akwa Ibom, Delta, Enugu, Cross River, Ondo ka iya rasa damar komawa kujerarsu a zaben 2027.
Har ila yau, Fasto Ayodele ya ce a Arewacin Najeriya ma akwai jihohi kamar Kaduna, da Zamfara da ya ce suna cikin haɗari, cewar The Guardian.
Ya ce:
“Wadannan gwamnoni dole su yi aiki tukuru da addu’a don samun nasara, ba za a tabbatar musu da wa’adi na biyu ba idan ba su yi ƙoƙari sosai ba.”
Fasto ya gargadi Akpabio da Sanata Ned Nwoko

Kara karanta wannan
Tsugune ba ta kare ba: Gwamna na iya rasa kujerarsa bayan barin PDP da ta kawo shi
Haka kuma ya ja kunnen Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ya kasance cikin shiri da addu’a, yana cewa kujerarsa na iya barazanar rasa ta.
Limamin ya kuma gargadi Sanata Ned Nwoko na jihar Delta da kada ya nemi kujerar gwamna yanzu, yana mai cewa, “Lokacinsa bai yi ba."
Ayodele ya ƙara cewa wasu daga cikin ’yan majalisar dattawa da wakilai ba za su dawo a 2027 ba saboda wasu matsalolin siyasa da shiri mara ƙarfi.
Fasto ya fadi abin da zai faru a 2027
Mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin kirista, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya gargaɗi Bola Tinubu ya tashi tsaye domin daƙile rikicin siyasa.
Malamin ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake hasashen abin da zai iya faruwa a zaben shugaban ƙasa mai zuwa a zaben shekarar 2027.
A wani faifan bidiyo, Ayodele ya ce matukar Tinubu da muƙarrabansa suka gaza yin abin da ya dace, za su fuskanci ƙalubale a zaɓe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
