Zaben Gwamna: APC Na da ‘Yan Takara 14 da Ke Son Karɓar Mulki daga PDP a Osun

Zaben Gwamna: APC Na da ‘Yan Takara 14 da Ke Son Karɓar Mulki daga PDP a Osun

  • Akalla 'yan siyasa 14 daga jam’iyyar APC sun bayyana niyyarsu ta kalubalantar Gwamna Ademola Adeleke a 2026
  • Daga cikin su akwai Otunba Iyiola Omisore, Omooba Dotun Babayemi, Bola Oyebanji, da Farfesa Rafiu Durodoye
  • Sai dai, jam'iyyar PDP ta ce ‘yan takarar APC “ba su da wani tasiri,” yayin da ita APC ke cewa za ta sake karɓar mulki a Osun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun – Rikicin siyasa a jihar Osun ya fara ɗaukar zafi yayin da akalla mutum 14 daga APC suka nuna sha'awar yin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar.

Wadannan 'yan takara 14, sun bayyana aniyarsu ta hambarar da Gwamna Ademola Adeleke na PDP a zaben gwamnan Osun da za a gudanar a 2026.

'Yan takara 14 sun nuna sha'awar yin takarar gwamna a zaben Osun na 2026.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adekele ya na kada kuri'arsa a zaben jihar. Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

Osun 2026: APC ta samu 'yan takara 14

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya yi albishir ga Shugaba Tinubu kan zaben 2027

Daga cikin fitattun ‘yan takarar akwai Otunba Christopher Iyiola Omisore, Hon. Bola Oyebamiji, Omooba Dotun Babayemi, da Farfesa Rafiu Durodoye, inji rahoton Leadership.

Sauran 'yan takarar sun haɗa da Dr. Akin Ogunbiyi, Hon. Benedict Adegboyega Alabi, Sanata Babajide Omoworare, da Sanata Mudashiru Hussain.

Sannan akwai Hon. Kunle Rasheed Adegoke, Mr. Babatunde Oralusi, da Dr. Peter Babalola, wadanda suka nuna sha’awa amma ba su bayyana hakan a hukumance ba.

‘Yan takarar sun fito daga sassa daban-daban na jihar — daga Osun ta Yamma akwai Oyebanji, Alabi, Ogunbiyi, Hussain, Babayemi, da Babalola, yayin da Omisore, Oralusi da Omoworare suka fito daga Osun ta Gabas, sannan Adegoke da Durodoye daga yankin Osun ta Tsakiya.

Osun: PDP ta yi watsi da ‘yan takarar APC

Sai dai jam’iyyar PDP ta ce ba ta damu da waɗannan ‘yan takara ba, tana mai kiran su da “‘yan siyasar marasa tasiri” da ba su kama kafar Gwamna Ademola Adeleke a farin jini da karbuwa ba.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Hon. Sunday Bisi, ya ce ayyukan da Gwamna Ademola Adeleke ya shimfida a jihar ne za su yi masa yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

'Tinubu zai fadi zaben 2027 duk da karfin APC,' Ministan Buhari ya fadi dalili

“Ayyukan Gwamna Adeleke sun taɓa rayuwar kowane ɗan Osun. Jama’a sun gamsu da ayyukansa, kuma hakan ne zai tabbatar da nasararsa."

- Hon. Sunday Bisi.

PDP ta ce 'yan takarar APC ba za su iya kayar da Gwamna Adeleke a zaben 2026 ba.
Taswirar jihar Osun da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

APC ta ce za ta karɓi mulkin jihar Osun

Shugaban jam’iyyar APC a Osun, Sooko Tajudeen, ya jaddada cewa jam’iyyar za ta lashe zaben 2026, tare da gargadin ‘yan takara da su 2karfafa ginshikin jam’iyya.

“Dole kowa ya yi aiki tukuru, har sai an yi zaben fitar da gwani, an samu dan takara guda. Manufarmu ɗaya ce — mu ceci jama’ar Osun daga gwamnatin PDP."

- Sooko Tajudeen.

Daga cikin masu neman takara, Farfesa Rafiu Durodoye, wanda yake malami a Amurka, shi ne na farko da ya kai ziyara ofishin jam’iyyar a Osogbo ranar 3 ga Yuni, 2025.

Na ƙarshe kuma shi ne Otunba Iyiola Omisore, wanda ya bayyana aniyarsa ranar 8 ga Oktoba, 2025, yana mai cewa:

“Ina da tabbacin samun kashi 90% na kuri’un fidda gwani — kuma zan lashe zaben jihar.”

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Adeleke

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun koli a Najeriya ta tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da ya gabata a 2022.

Kara karanta wannan

Wasu manyan 'yan siyasa a Arewacin Najeriya sun fice daga jam'iyyun APC da PDP

Tsohon gwamna Oyetola ya ɗaukaka kara zuwa Kotun koli, inda ya kalubalanci nasarar gwamna Ademola Adeleke.

Alkalin da ya jagoranci shari'ar yace Oyetola ya gaza gamsar da Kotu zargin da ya yi na aringizon kuri'a ranar zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com