'Tinubu Zai Fadi Zaben 2027 duk da Karfin APC,' Ministan Buhari Ya Fadi Dalili
- Tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya ce APC na nuna rashin kwarin gwiwa ta hanyar danniya ga ‘yan adawa
- Sakataren ADC na kasa, ya ce jam’iyyarsu ce za ta amfana da rashin farin jinin da APC ke fama da shi a zaben 2027
- Tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da tsohon minista Bolaji Abdullahi, sun ce ADC ta shirya karɓar mulki a zaben gaba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ilorin – Tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya zargi jam’iyyar APC da shiga firgici, gami da rasa kwarin gwiwa kan zaben 2027.
A cewar Aregbesola, wanda shi ne sakataren jam'iyyar ADC na kasa, APC ta dawo muzgunawa ‘yan adawa da wadanda suka saba da ra’ayinta.

Source: Twitter
"APC ta rasa farin jini" - Aregbesola
Aregbesola ya bayyana haka ne a Ilorin, yayin tattaunawa da manema labarai bayan kaddamar da sabuwar sakatariyar ADC da ke titin Basin Road, Ilorin, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Da APC na da tabbaci kan karfinta, da ba za ta dinga tsoratar da ‘yan adawa a ko’ina ba. A yanzu sun koma danne 'yan adawa daga Legas zuwa Kebbi da Kaduna, saboda tsoro.”
- Rauf Aregbesola.
Ya ce irin wannan halayya ta nuna cewa APC ta rasa farin jini, kuma ADC ce za ta amfana da fushin da jama’a ke yi da jam'iyyar a zabukan 2027.
Aregbesola ya bayyana cewa:
“Jam’iyyar da ta san tana da farin jini ba za ta nuna damuwa har haka ba. Amma APC ta san cewa jama’a sun gaji da ita, kuma ADC ce za ta karɓi ragamar mulki a Najeriya da jihohi da dama."
"ADC ce za ta karbi mulki a 2027' - Abdulfatah
A nasa bangaren, tsohon gwamnan Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed, wanda ya bar PDP zuwa ADC, ya ce jam’iyyarsu ta shirya don karɓar mulki a 2027, inji rahoton Punch.
“Jam’iyyar ta shirya kuma za ta ba marar da kunya. Wannan alama ce ta sabon babin siyasa a Kwara, kuma kai da ni ne ginshikin wannan sabuwar tafiya,” in ji Abdulfatah.
Ya kara da cewa jam'iyyar ADC ce za ta ba 'yan Najeriya sabon yakini ta hanyar shugabanci nagari, wanda zai kai kasar tudun-mun-tsira.

Source: Facebook
'PDP ta zama marainiya a siyasa’ - Bolaji
Shi ma Mai magana da yawun ADC na kasa kuma tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Mallam Bolaji Abdullahi, ya caccaki jam’iyyar PDP, yana mai cewa ta rasa dukkan tasirinta a siyasar Najeriya.
“PDP yanzu ta zama marainiya a siyasa. Ba ta da tasiri, kuma ba za ta iya jagorantar sabuwar tafiyar da ‘yan Najeriya ke bukata ba,” in ji Bolaji.
Ya ce ADC ce kawai jam’iyyar da ke dauke da sababbin shirye-shirye da ingantaccen tsari, don dawo da aminci, gaskiya da ci gaba a tsarin mulkin kasar.
'APC ta jawo yunwa, rashin tsaro' - Aregbsola
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya ce Jam’iyyar APC ta gaza cika alkawura da ta daukar wa Najeriya.
Aregbesola, wanda shi ne sakataren ADC na kasa, ya ce jam'iyyarsu ce za ta iya ceto Najeriya daga talauci, tsadar rayuwar da ake ciki a kasar.
Tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da tsohon minista, Bolaji Abdullahi, sun yaba da karuwar karfin ADC, suna masu cewa ita ce za ta lashe zabe a 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

