2027: Peter Obi Ya Magantu kan Fafatawa da Atiku domin Neman Tikitin ADC

2027: Peter Obi Ya Magantu kan Fafatawa da Atiku domin Neman Tikitin ADC

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya ce a shirye yake ya fafatwa da kowa domin neman tikitin takara
  • Obi ya ce bai ji tsoron maganar cewa Atiku Abubakar zai karɓe tikitin ADC ba, yana kiransa ɗan uwa
  • Ya jaddada cewa zai tsaya takara a 2027, yana mai cewa cancanta, iya aiki da gaskiya ne su jagoranci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya yi magana kan neman takitin takarar shugaban kasa.

Obi ya karyata jita-jitar da ke yaduwa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na shirin karɓe tikitin a ADC.

Obi ya yi magana kan neman takara d a Atiku
Tsohon gwamna Peter Obi da Atiku Abubakar. Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Obi ya magantu kan fafatawa das Atiku

Peter Obi ya yi wannan bayani ne a wata hira da PUNCH yayin ziyararsa makarantar firamare ta LEA, Kapwa, Abuja.

Kara karanta wannan

Wike na shirin yin takara da Tinubu a 2027? An ji gaskiyar zance

Peter Obi ya ce bai jin tsoron duk wani yunkurin siyasar Atiku ba, yana mai bayyana shi a matsayin “babban ɗan uwa kuma jagora mai girmamawa.”

Ana alakanta wannan jita-jita da rahotannin cewa wasu magoya bayan Atiku daga jam’iyyar PDP sun fara sauya sheƙa zuwa cikin haɗin gwiwar ADC, abin da ya tayar da hankalin magoya bayan Obi.

Fargabar ta ƙara ƙaruwa bayan Atiku ya bayyana cewa ba zai janye wa kowa ba sai dai idan an doke shi a zaɓen fidda gwani na ADC.

Abin da Obi ya sanya a gaba

Sai dai Peter Obi ya ce babu dalilin tsoro, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwar da ake ginawa ba takaddama bace, amma yunƙuri ne na ceto ƙasa daga halin da take ciki.

A cewarsa:

“Atiku ɗan uwa ne da nake girmamawa ƙwarai. Ni ɗan jam’iyyar LP ne, kuma ina cikin haɗin gwiwar da ake shirya ta ADC don zaben shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Zaben 2019: Yadda Akpabio ya yi karyar an yi masa magudin zabe a gaban Sanatoci

“Zan iya tabbatar muku cewa wasu jam’iyyu da mutane da dama za su kasance cikin wannan haɗin gwiwa. Za mu haɗa kai a matsayin ‘yan ƙasa ɗaya. Wannan shi ne imanin da nake da shi."

Peter Obi ya ce bai jin tsoron fafatawa da kowa a neman takara
Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Peter Obi. Hoto: Peter Obi.
Source: Facebook

Alwashin da Peter Obi ya sha kan takara

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma nuna shirin sake tsayawa takara, ko dai a ƙarƙashin ADC ko wata jam’iyya, yana mai cewa abin da ya kamata a duba shi ne iya aiki, cancanta da gaskiya a shugabanci.

“Ina iya tsayawa takara, kuma tabbas zan tsaya. Jama’a za su duba wanda ya fi cancanta, wanda yake da ƙwarewa da ƙarfin iya aiki. Na yi imani cewa ni na dace.

“Ina da ƙwarewar aiki. Na faɗa sau da dama cewa a cikin shekaru huɗu, zan iya sauya tafiyar Najeriya zuwa hanya mai kyau,”

- Peter Obi ya

Legit Hausa ta yi magana dan ADC

Wani dan ADC a Gombe, Muhammad Salisu Adamu ya bayyana kwarin guiwa kan yiwuwar samun nasararsu a zaben 2027.

"Idan har za a cire son rai wurin zaben fitar da gwani tsaknin dukan yan takara, to muna kwarin guiwar samun nasara a babban zabe."

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin kayar da Paul Biya, ana kone kone a Kamaru kan 'magudin zabe'

- Muhammad Salisu Adamu

Adamu ya ce dole duka yan takara su tsaya tsayin daka domin cire son kai saboda kawar da gwamnatin APC.

LP ta roki Atiku kan takara

Kun ji cewa jam'iyyar LP ta mika kokon bararta ga tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar LP ta bukaci.

Atiku ya hakura da burinsa na yin takara don marawa Peter Obi baya a zaben shugaban kasa na 2027.

Hakazalika ta bayyana matsayarta kan batun cewa tsohon 'dan takaran zai hakura da neman mulkin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.