Wasu Manyan 'Yan Siyasa a Arewacin Najeriya Sun Fice daga Jam'iyyun APC da PDP
- Manyan jiga-jigai a PDP da APC a jihar Filato sun fice daga jam’iyyunsu saboda rashin gaskiya da rushewar akidojin siyasa
- Nde Isaac Wadak ya bar PDP, yana mai korafin rashin bin tsarin dimokuradiyya da watsi da ƙa’idojin kafa jam’iyyar
- Chief Robert Taple na APC shi ma ya yi murabus, inda ya ce yanzu zai rika ba da shawarwarin kawo ci gaban Filato
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Jam'iyya mai mulki a kasa, APC da kuma jam'iyya mai mulki a Filato, watau PDP, sun gamu da fiewar wasu manyan kusoshinsu a jihar.
An ruwaito cewa, Nde Isaac Wadak, wanda ya shafe shekaru fiye da 25 yana yiwa PDP hidima, da Chief Robert Taple na APC, sun fice daga jam'iyyunsu.

Source: Twitter
Nde Isaac Wadak ya fice daga PDP
A wani yanayi da ya girgiza siyasar Filato, Nde Isaac Wadak, wanda shi ne tsohon shugaban cibiyar (CITN), ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar PDP, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasikar da ya aika wa shugaban PDP na Kabwir Pada Ward a karamar hukumar Kanke, Wadak ya bayyana cewa jam’iyyar ta kauce daga akidojin da aka kafa ta a kansu.
Wadak ya ce:
“Abin takaici ne yadda akidoji da falsafar da PDP ta ginu a kansu ke lalacewa. Aminci da gaskiya sun mutu, ana ba da lada ga masu kwaɗayi da wadanda ba su cancanta ba.”
Wadak, wanda yake mamba ne a cibiyar FCTI, ya bayyana cewa ya kasance cikin tawagar Redemption Team ta tsohon Gwamna Jonah Jang da kuma cikin masu tallafa wa Gwamna Caleb Mutfwang a zaben 2023.
Sai dai ya ce, lamirinsa da imanin sa sun hana shi ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ke fuskantar rugujewa, don haka ya yanke shawarar ficewa gaba ɗaya.
Chief Taple ya bar APC don samun ‘yanci
Haka kuma, Chief Robert Taple, wani jigon APC, ya sanar da murabus dinsa ta wata wasika da ya kai ofishin jam’iyyar a Kalwa House, Jos, ta hannun shugaban gundumarsa na Lankan a karamar hukumar Pankshin.
A cikin wasikar, Taple ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin nesa da jam’iyyar domin ya samu damar bayar da shawarwari cikin ‘yanci don ci gaban jihar Filato da Najeriya baki ɗaya.
Ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi ya yi hidima ba tare da wani abin kunya ba.

Source: Original
APC ta kafa kwamiti karɓar sababbin mambobi
A halin yanzu, jam’iyyar APC ta kafa kwamiti karkashin Elder Pam Gyang domin karɓar sabbin mambobi da suka nuna sha’awa shiga jam’iyyar a ranar Oktoba 30, inji rahoton Channels TV.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa yana karɓar kiran waya kullum daga mutane da ke son komawa jam’iyyar, yana mai cewa hakan alama ce ta farfadowar jam’iyyar a jihar Filato.
'APC za ta kwace Filato a 2027' - Minista
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Nentawe Yilwatda (lokacin da yake minista) ya ce PDP ba za ta ci gaba da mulki a Filato ba, don haka APC za ta karɓi mulki a 2027.
Farfesan wanda a yanzu shi ne shugaban APC na kasa, ya ce jam'iyyarsa ta APC ta shirya kwace mulki daga hannun Caleb Mutfwang.
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaɓen 2027, ya na mai cewa gwamnatinsa ta samar da tsaro a jihar Filato da kewaye.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


