ADC Ta Yi Babban Kamu, Tsohon Shugaban PDP Ya Yi Murabus bayan Shekaru 22

ADC Ta Yi Babban Kamu, Tsohon Shugaban PDP Ya Yi Murabus bayan Shekaru 22

  • ADC mai hamayya a Najeriya ta yi babban kamu bayan ficewar tsohon shugaban PDP na Kwara daga jam’iyyarsa
  • Hon. Babatunde Mohammed wanda ta taba zama kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, ya bayyana ficewarsa daga PDP bayan shekaru 22
  • Mohammed ya ce matakin da ya dauka na barin PDP ya zama wajibi saboda dalilai na kashin kansa inda ya tabbatar da shiga ADC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ci gaba da fuskantar matsaloli musamman na rashin 'ya'yanta da take yi a kullum.

A yau ma, tsohon shugaban PDP a jihar Kwara ya yi murabus daga jam'iyyar PDP bayan shafe shekaru fiye da 20 a cikinta.

Tsohon shugaban PDP ya bar ta zuwa ADC
Tsohon shugaban PDP, Hon. Babatunde Mohammed. Hoto: Kamaldeen Adeyemi Ajibade.
Source: Facebook

PDP ta rasa tsohon shugabanta a Kwara

Rahoton Leadership ta ce Hon. Babatunde Mohammed ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa ADC a yau Asabar 18 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Yaron Jonathan da ya taba zama 'dan majalisa ya watsar da PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed ya ce ya yanke shawara haka ne bayan shekaru 22 da kasancewa cikinta, inda ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne saboda dalilai na kashin kai.

Mohammed, wanda ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar, ya bayyana ficewarsa a wata wasika da ya aikawa shugaban PDP na mazabar Agunjin a karamar hukumar Ifelodun,

PDP ta rasa tsohon shugabanta a Kwara
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Tsohon shugaban PDP ya fadi sabuwar jam'iyyarsa

Har ila yau, ya tabbatar da cewa yanzu ya shiga jam’iyyar hadaka ta jam'iyyar ADC wanda gungun yan adawa suka hada karfi da karfe domin inganta ta.

Wasikar murabus ɗin Mohammed mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Oktoba, 2025, ta ce:

“Wannan wasika ce ta sanar da ku a hukumance cewa na yi murabus daga jam’iyyar PDP daga ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025.
“Na shiga jam’iyyar PDP tun a shekarar 2002, shekaru 22 da suka gabata, ba tare da na taɓa barinta ko da rana ɗaya ba. Amma dalilin barina jam’iyyar abu ne na kashin kai kawai.

Kara karanta wannan

Wike na shirin yin takara da Tinubu a 2027? An ji gaskiyar zance

“Ina godiya ƙwarai ga shugabannin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da mambobi saboda goyon bayansu da haɗin kansu, musamman a lokacin da nake shugabancin jam’iyyar a jihar.”

A wata tattaunawa ta wayar tarho da yan jarida, Mohammed ya ce ya riga ya yi abin da ya kamata a PDP, kuma yanzu lokaci ya yi da zai bar ta, cewar Daily Post.

A martanin PDP ta bakin sakataren yada labaranta, Olusola Adewara, jam’iyyar ta ce ta san da barin tsohon shugaban, amma hakan ba zai shafi nasarorinta ko karfinta a siyasar jihar ba.

Tsohon hadimin Jonathan ya bar PDP zuwa APC

A wani labarin, tsohon hadimin Goodluck Jonathan ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan shafe shekaru a cikinta.

Tsohon dan majalisa a jihar, Dr. Waripamo-owei Dudafa ya fice daga PDP tare da komawa APC mai mulkin Najeriya domin ba da ta shi gudunmawa.

Ya ce rikice-rikicen PDP sun sa ya fice daga jam’iyyar inda ya bayyana cewa matsalolin cikin gida da rashin zaman lafiya na daga cikin dalilansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.