Yadda Gwamnatin APC Ta Jawo Yunwa da Matsalar Tsaro a Najeriya, ADC Ta Fasa Kwai

Yadda Gwamnatin APC Ta Jawo Yunwa da Matsalar Tsaro a Najeriya, ADC Ta Fasa Kwai

  • Tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya ce Jam’iyyar APC ta gaza cika alkawura da ta daukar wa Najeriya
  • Ya bayyana cewa ADC ce kawai jam’iyyar da za ta iya ceto Najeriya daga talauci, tsadar rayuwar da ake ciki a kasar
  • Tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, da tsohon minista, Bolaji Abdullahi, sun yaba da karuwar karfin ADC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Tsohon gwamnan jihar Osun kuma sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola, yi magana kan halin da Najeriya take ciki.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya zargi APC da gaza tafiyar da mulki da kyau, yana mai cewa jam’iyyar ta jefa Najeriya cikin yunwa, tsadar rayuwa, da rashin tsaro.

Jam'iyyar ADC ta ce gwamnatin APC ce ta jawo yunwa, talauci da rashin tsaro a Najeriya.
Kusoshin adawa a Najeriya sun kaddamar da jam'iyyar ADC matsayin dandalin hadaka a Abuja. Hoto: @atiku
Source: Facebook

"APC ta jefa mutane a talauci' - Aregbesola

Aregbesola ya yi wannan magana ne a ranar Asabar yayin kaddamar da ofishin ADC na jiha a Ilorin, jihar Kwara, a cewar rahoton jaridar Punch.

Kara karanta wannan

ADC ta yi babban kamu, tsohon shugaban PDP ya yi murabus bayan shekaru 22

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen taron, sakataren ADC ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza cika alkawuranta na ci gaba da yin adalci ga 'yan Najeriya.

“Yunwa ta mamaye ƙasa, mulki ya zama hanyar tara dukiya da tsoratar da jama’a. Talaka yana cikin azaba saboda gazawar shugabannni a karkashin APC."

- Ogbeni Rauf Aregbesola.

Ya kuma zargi jam’iyyar da hana ‘yancin ra’ayi da amfani da karfin gwamnati don murkushe ‘yan adawa.

'ADC ce zabin jama’a a 2027' – Aregbesola

Aregbesola ya kara da cewa:

“Da APC na da tabbaci kan karfinta a kasar nan, da ba ta tsoratar da ‘yan adawa a ko’ina ba."

A cewarsa, ADC jam’iyya ce da aka kafa bisa tsari da riko da gaskiya, wacce za ta kasance amintacciya ga ‘yan Najeriya, bayan sun gaji da mulkin APC.

“Kiyayyar da ‘yan Najeriya ke nuna wa jam’iyya mai mulki ta fito fili yanzu. Jam’iyyar da za ta amfana da wannan rashin farin jini ita ce ADC."

Kara karanta wannan

Yaron Jonathan da ya taba zama 'dan majalisa ya watsar da PDP zuwa APC

- Ogbeni Rauf Aregbesola.

Aregbesola ya ce jam'iyyar ADC ce za ta fitar da Najeriya daga kangin talauci da matsin tattali da take ciki.
Hoton tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola. Hoto: @raufaregbesola
Source: Twitter

Tsohon gwamna ya yaba wa ADC

A nasa bangare, tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya ce bullar ADC a jihar alama ce ta sabon salo a siyasar jihar.

“Wannan sabuwar hanya ce ta siyasa. ADC za ta zama jam’iyyar da za ta ba da fifiko ga muradin ‘yan Kwara,” in ji Abdulfatah.

Shi ma tsohon ministan matasa da wasanni, Bolaji Abdullahi, wanda shi ne mai magana da yawun ADC na kasa, ya bayyana PDP a matsayin “matacciyar jam’iyya da ke jiran jana’izarta”, yana mai cewa ADC ita ce kadai babbar jam’iyyar da za ta iya kalubalantar APC.

Ya kuma koka kan karuwar rashin tsaro a yankunan karkara na jihar Kwara, yana mai cewa:

“Mutanenmu ba sa iya yin noma cikin kwanciyar hankali. Ya kamata gwamnati ta dauki mataki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”

'Za mu cire Tinubu daga Aso Villa' - Aregbesola

Tun da fari, mun ruwaito cewa, sakataren ADC, Rauf Aregbesola, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu za ta hambarar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

APC za ta ci gaba da raunata 'yan adawa, Yilwatda ya fadi manyan ADC da za su koma jam'iyyar

Rauf Aregbesola ya bayyana cewa jam'iyyar ADC za ta kwace Lagos da fadar gwamnati ta Abuja a babban zaɓen 2027 da ke tunkarar kasar.

An kuma samu wata ƙungiya mai suna Conscience Forum daga LP ta koma ADC a lokacin da ta cika shekaru 25 da kafuwa don tabbatar da sauyi a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com