Wike Ya Burma Matsala bayan Sakin Baki, an Bukaci Diyyar N20bn daga gare Shi

Wike Ya Burma Matsala bayan Sakin Baki, an Bukaci Diyyar N20bn daga gare Shi

  • Tsohon ɗan takarar gwamna na APC ya taso ministan Abuja a gaba kan wasu kalamansa inda ya nemi diyya
  • Jigon APC, Tonye Cole ya bukaci N20bn da neman afuwa daga Nyesom Wike ko ya dauki mummunan mataki a kai
  • Lauyansa, Jibrin Okutepa, ya ce Wike ya kira Cole da ɓarawo yayin hira da yan jaridu wanda aka watsa a duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Tsohon dan takarar gwamna a jihar Rivers ya bukaci ministan Abuja, Nyesom Wike ya nemi afuwarsa.

Tonye Patrick Cole wanda ya yi takara a jam’iyyar APC a jihar Rivers, ya bukaci biliyan 20 daga Nyesom Wike.

Jigon APC ya bukaci diyyar N20bn daga Wike
Tsohon dan takarar gwamna a Rivers, Tonye Cole da Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Wike, Tonye Cole.
Source: Facebook

Zargin da ake yi wa ministan Abuja, Wike

Rahoton TheCable ya ce Cole ya dauki matakin ne bisa kalaman batanci da Wike ya yi gare shi wanda ya bata masa suna a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Matsala ta tunkaro Gwamna Diri kan ficewa daga PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyansa, Jibrin Okutepa, ya aika da wasiƙa ranar 8 ga Oktobar 2025, inda ya zargi Wike da yin maganganun da suka ɓata suna yayin hira a Channels TV ranar 18 ga Satumba, 2025.

A cewar wasiƙar, Wike ya kira Cole da ɓarawo, yana zarginsa da satar dukiyar jihar da kuma sayar da gas ɗin Rivers da ya ya kai darajar dala miliyan 308.

Yadda Wike ya batawa jigon APC suna

Lauyan ya ce wannan hira ta haifar da mummunan tasiri ga sunan Cole tunaninsa da martabarsa tare da rasa amincewar jama'a da abokan hulɗa.

Okutepa ya ƙara da cewa an watsa kalaman Wike a ƙasa da ƙetare ta hanyar gidan talabijin, inda har yanzu ana iya kallon su a YouTube.

Ya bayyana cewa hakan na ci gaba da cutar da martabar Cole, kuma Wike ya aikata hakan cikin rashin gaskiya da keta dokokin ɗabi’a.

An bukaci Wike ya fito duniya ya ba da hakuri kan kalamansa
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin hira da yan jaridu. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Twitter

Abin da ake bukata daga Nyesom Wike

Kara karanta wannan

Tofa: Peter Obi ya maka sanannen lauya a kotu, yana neman diyyar Naira biliyan 1.5

Tonye Cole ya buƙaci Wike ya janye kalamansa, ya ba da haƙuri a rubuce da kuma a shirye-shiryen talabijin da jaridu uku cikin kwanaki 14.

Haka kuma ya buƙaci diyya ta N20 biliyan da alƙawarin Wike ba zai sake yin irin wannan kalaman ba.

Lauyoyin sun kuma yi gargaɗin cewa za su ɗauki matakin shari’a idan ba a bi umarnin ba domin koya masa darasi kan fade-fade da kuma sanin abin da zai rika furtawa.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, Wike ko na kusa da shi ba su yi martani kan abin da ake zargin ministan a kai ba, cewar Daily Post.

Wike ya taba wadanda suka koma APC

Mun ba ku labarin cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan sauya shekar da wasu 'yan siyasa ke yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Wike ya bayyana masu yi sukar salon siyasarsa yanzu su ne su ke komawa jam'iyyar APC mai mulki.

Miinistan ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan manufofin da ya ke aiwatarwa a gwamnatinsa wanda ke jawo hankalin yan adawa a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.