Surukar Akpabio Ta Ballo Ruwa, Ta Jingina Shugaban Majalisa da Kashe Jama'a a Akwa Ibom
- Sabon rikici ya nufo Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Obot Akpabio daga gidansa, inda ake zarginsa da kisan kai
- Pat Akpabio, kanwar mai dakinsa ta zargi Akpabio da hannu a kisan gilla da aka yi wa wasu mutane a lokacin yana Gwamna
- Ta yi barazanar fito da bayanai a kan zarge-zargen da ta yi, kuma tuni ofishin Shugaban Majalisa ya yi mata martani
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Akwa Ibom – Pat Akpabio, kanwar matar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, na shirin jefa mijin yayarta a cikin matsala.
Pat ta yi zargin cewa Godswill Akpabio ba mutumin kirki ba ne, domin yana da hannu dumu-dumu a kisan wasu bayin Allah a Akwa Ibom lokacin yana Gwamna.

Source: Facebook
A wani faifan bidiyon da ta wallafa a Facebook, Pat ta ce baya ga kashe mutane yana Gwamna, Akpabio ya na da masaniya a kisan wadansu bayin Allah bayan ya shiga majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pat ta caccaki Godswill Akpabio
Premium Times ta wallafa cewa Pat, wacce malama ce kuma ‘yar kasuwa, tana auren Ibanga Akpabio, wanda ake gani a matsayin wanda ya taimaka wa Godswill Akpabio a siyasa.
Ta ce:
“Za ku ga sakayya a kan duk mutanen da ka kashe lokacin da ku ke gwamna da wadanda ku ka kashe yanzu da ka ke majalisa.”
Har wa yau, Pat ta bayyana cewa Akpabio ya ci amanar mutane da dama a Akwa Ibom da suka taimake shi.
Daga cikin mutanen da Pat ke ganin Akpabio ya ci amanarsu akwai Umana Okon Umana, Nsima Ekere, Akan Udofia da Bassey Albert.
Ta ce ya manta da alherin da mutane suka masa, kuma ta sha alwashin kalubalantar sa a zaben majalisar dattawa na 2027.

Source: Facebook
Pat ta karada barazanar cewa tana da karin bayani da za ta fitar idan bai mayar da martani yadda ya kamata ba.
Ta ce:
“Na tsaya maka a 2019, ban karɓi ko Naira goma daga gare ka ba. Amma yau kana da bakin cewa kai ka gina ni?”
Pat ta kuma shawarci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya bi a hankali da kuma taka tsantsan a alakarsa da Akpabio.
Martanin Akpabio ga surukarsa
Mai magana da yawun shugaban majalisar, Eseme Eyiboh, ya mayar da martani ga kalaman Pat da cewa, ya kamata ta kai karar irin wannan zargi ga hukumomin tsaro.
Ya ce:
“Kisan kai batu ne da doka ta dauka da muhimmanci. Duk wanda ke da shaida ya kamata ya gabatar da ita.”
Eyiboh ya kara da cewa, Akpabio mutum ne mai hakuri da daraja a danginsu, kuma bai da lokacin kula da irin wadannan zarge-zarge.
Dangane da batun yawaitar kashe-kashe a lokacin mulkin Akpabio, Eyiboh ya ce matsalar rashin tsaro ba wai a Akwa Ibom kadai take ba.
Ya ce:
“Ba za a ce shugaban kasa Tinubu ne ke kisa ko bama-bamai ba saboda gwamnatinsa ce ta ke mulki. Haka kuma ba daidai ba ne a danganta kashe-kashe da Akpabio kawai.”
Mai Magana da yawun Shugaban Majalisa ya yi zargin cewa Pat na neman ta ja hankali ne kawai, kuma Godswill Akpabio ba zai saurare ta ba.
Akpabio ya yi wa 'yan adawa shagube
A baya, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi wa jam’iyyun adawa shagube yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2025.
Sanata Akpabio ya bayyana cewa jam’iyyun adawa na kara fuskantar koma baya, ganin yadda 'ya'yansu ke ci gaba da barinsu suna komawa jam’iyyar APC da ke mulkin kasa.
Shugaban Majalisar ya fadi hakan ne a yayin da Sanata Kelvin Chukwu, dan majalisar da ke wakiltar Enugu ta Gabas, ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar LP zuwa jam’iyyar APC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


