Fadar Shugaban Kasa Ta Cika Baki kan Tazarcen Tinubu a Zaben 2027
- Fadar shugaban kasa ta tabo batun tazarcen Mai girma Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 duk da ba a buga gangar siyasa ba
- Ta bayyana cewa shugaban kasan ya yi ayyukan da za su sanya shi doke abokan adawa, ya sake lashe zabensa cikin sauki
- Hakazalika ta tabo batun 'yan siyasar da za su iya kalubalantar shugaban kasan don darewa kan madafun ikon Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta sake jaddada cikakken kwarin gwiwarta kan nasarar sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Fadar shugaban kasan ta bayyana cewa babu wani dan siyasa a halin yanzu da zai iya kalubalantar Mai girma Bola Tinubu.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce mai ba shugaban kasa shawara kan yada manufofi, Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 14 ga watan Oktoban 2025 a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi magana ne yayin wani taron tattaunawa da kungiyoyin masu goyon bayan Tinubu sama da 100 daga sassa daban-daban na kasar nan, rahoton The Punch ya tabbatar da labarin.
Yayin da yake jawabi a wajen, Daniel Bwala ya ce nufin taron shi ne karfafa hadin kai tsakanin fadar shugaban kasa da kungiyoyin goyon bayan Tinubu a matakin kasa, gabanin zaben 2027.
A cewarsa, manufofin tattalin arziki da shirye-shiryen ci gaban da Tinubu ya aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun dawo da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin kasa, lamarin da ke tabbatar da cewa zai yi nasarar sake lashe zabe cikin sauki.
“Babu wani dan siyasa a yau a Najeriya da zai iya kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Mun fito daga ‘Renewed Hope’ yanzu muna cikin matakin ‘farfadowa,’ kuma dole talakawa su ji wannan ci gaban a rayuwarsu."
- Daniel Bwala
Yayin da yake jaddada nasarorin gwamnati, Bwala ya ce sake fasalin tattalin arziki da Tinubu ya gudanar cikin shekaru biyu ya fara nuna sakamako a sassa da dama, ciki har da makamashi, noma, gina ababen more rayuwa da samar da ayyukan yi.
“Tuni mun fara gani a kasa. Duk lokacin da muka fita, za mu ga ci gaba a bangaren tattalin arziki, tsaro, ilimi, da noma. Kungiyoyin nan za su ci gaba da yada wannan sakon."
- Daniel Bwala

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya samu yabo
A nasa bangaren, tsohon dan majalisar tarayya Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, ya yabawa jagorancin Tinubu, yana bayyana shugaban kasan a matsayin wanda ya shimfida tubalin ci gaba mai dorewa.
“Ko ana so ko ba a so, Shugaba Tinubu zai sake lashe zabe a 2027. Ba mu kai inda muke so ba, amma muna kan hanyar samun ci gaba, kuma shugaban kasa na kokarin hanzarta wannan ci gaban."
- Ehiozuwa Johnson Agbonayinma
Ya kuma yaba da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi, yana mai cewa matakin ya an saki makudan kudi ga gwamnatocin jihohi domin gudanar da ayyukan raya karkara.
Dukkanin masu jawabin sun bukaci kungiyoyin goyon bayan gwamnati da su ci gaba da wayar da kai kan manufofin gwamnatin, tare da karfafa hadin kai a tsakanin yankuna da jam’iyyun siyasa daban-daban.
Wike ya magantu kan sabani da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan batun samun sabani tsakaninsa da Mai girma Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Da gaske sabon shugaban INEC na cikin lauyoyin Tinubu a zaben 2023? an samu bayanai
Wike ya bayyana cewa babu wani abu da ya taba kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsa da shugaban kasan.
Ministan ya bayyana cewa rahotannin karya ne kawai ake yadawa kan batun alaka ta yi tsami tsakaninsa da Mai girma Bola Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

