'Babu Sauran Hamayya,' Jam'iyyar APC Ta Tsaida Ɗan Takararta a Zaben Gwamnan Ekiti

'Babu Sauran Hamayya,' Jam'iyyar APC Ta Tsaida Ɗan Takararta a Zaben Gwamnan Ekiti

  • Jam’iyyar APC ta amince da Gwamna Biodun Oyebanji a matsayin dan takararta a zaben gwamnan jihar Ekiti na 2026
  • Oyebanji ya samu nasarar zama dan takarar APC ne bayan da sauran 'yan takara suka janye, suka mara masa baya
  • APC ta ce ta sanar da INEC tsarin da ta yi amfani da shi na fitar da dan takara, kamar yadda dokar zaɓe ta 2022 ta tanada

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ekiti – Jam’iyyar APC ta ta amince ta tsaida ɗan takarar gwamnan jihar Ekiti ba tare da hamayya ba, sabanin tsarin zaben fitar da gwani na kato-bayan-kato.

Yanzu dai Gwamna Biodun Oyebanji ne ya samu tikitin takarar gwamnan Ekiti a zaben da za a gudanar a 2026 na APC, bayan sauran 'yan takara sun janye masa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama miji da mata masu safarar makamai ga ƴan ta'adda a jihohin Arewa

Gwamna Biodun Oyebanji ya zama dan takarar gwamnan jihar Ekiti
Hoton gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya na magana a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Ado-Ekiti. Hoto: @biodunaoyebanji
Source: Twitter

Mai magana da yawun jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya sanar da wannan matsayar a sanarwar da ya fitar a ranar Talata, a cewar rahoton The Cable.

APC ta fitar da dan takarar gwamnan Ekiti

Felix Morka ya bayyana cewa an tsayar da dan takarar ba tare da hamayya ba, bayan janyewar Atinuke Oluremi Omolayo, wadda ita ce kawai ta rage a cikin masu takara da aka tantance.

A cikin wasikar da ta aika wa jam’iyyar, Omolayo ta sanar da janyewarta daga takara tare da bayyana goyon bayanta ga Gwamna Oyebanji.

Mai neman takarar ta bayyana cewa tana goyon bayan duk wani tsari da APC za ta ɗauka bisa tanadin dokar zaɓe ta 2022 da kundin tsarin jam’iyyar.

Felix Morka ya bayyana cewa canjin daga tsarin zabe na kato-bayan-kato zuwa zabe marar hamayya ya riga ya samu amincewar hukumar INEC ta hanyar wata wasika da aka aike mata a ranar 13 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP a Enugu ya sauya sheka, ya hade da Tinubu a APC

Tsarin zaben dan takarar gwamnan Ekiti

Ya kara da cewa wannan mataki ya yi daidai da sashe na 84 (9) da (11) na dokar zaɓe ta 2022, wanda ya ba jam’iyyu damar yin tsayar da dan takara ba tare da hamayya ba idan aka samu yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki.

Jam’iyyar APC ta kuma fitar da jadawalin shirye-shiryenta na cikin gida kan zaben Ekiti, wanda zai fara da zaɓen wakilai a ranar 25 ga Oktoba, 2025, inji rahoton The Nation.

Bayan zaben wakilai, sai kuma karɓar ƙorafe-ƙorafe a ranar 26, ga Oktoba, 2025 kafin babban taronta a ranar 27 ga Oktoba, 2025 domin tabbatar da dan takararta.

Gwamnan Ekiti, ya zama dan takarar gwamnan Ekiti na jam'iyyar APC
Hoton gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji yana jawabi a wani taron kananan hukumomi a Ado Ekiti. Hoto: @biodunaoyebanji
Source: Twitter

APC ta dakatar da mutane 2 daga takara

Felix Morka ya yaba da kishin jam’iyya da Omolayo ta nuna, inda ya yi kira ga dukkan ‘yan jam’iyyar a Ekiti su haɗa kai domin tabbatar da nasararta a zaben gwamna na Yunin 2026.

A ranar 9 ga Oktoba, jam’iyyar ta dakatar da Kayode Ojo da Abimbola Olawumi daga takarar gwamna, ba tare da bayyana dalilai ba.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya fadi illar da ficewar Farfesa Pantami za ta yi wa jam'iyyar

INEC ta sanya ranar zaben jihar Ekiti

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta sanar da cewa za ta gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 20 ga Yuni, 2026.

Hukumar INEC ta kuma amince jam’iyyun siyasa su fara gudanar da zaɓen fitar da gwani a jihar Ekiti daga ranar 20 ga Oktoba zuwa 10 ga Nuwamba, 2025.

Daga nan ne za su tura sunayen ‘yan takara zuwa shafin yanar gizo na INEC kafin 22 ga Disamba, 2025, wanda zai ba hukumar damar gudanar da zaben a Yunin 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com