Gwamna Ya Kwantar da Hankalin 'Yan PDP kan Yawan Ficewa daga Jam'iyyar, Ya Yi Albishir
- Ana ci gaba da samun sauya shekar wasu manyan jiga-jigai daga jam'iyyar PDP zuwa wasu jam'iyyun siyasa
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karfafa gwiwar mambobin PDP kan yawan ficewar da ake yi daga jam'iyyar
- Makinde ya bukace su da kada su karaya domin jam'iyyar adawar za ta farfado ta dawo kan turbar da ta dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan yawan sauya shekar da ake yi daga jam'iyyar PDP zuwa wasu jam'iyyu.
Gwamna Makinde ya shawarci mambobin PDP da kada su karaya ko su damu da yawan ficewar da wasu 'yan siyasa ke yi daga jam’iyyar a 'yan kwanakin nan.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce Makinde ya yi wannan jawabi ne a Abuja ranar Litinin yayin taron farko na karamin kwamitin sufuri na kwamitin shirya babban taron jam’iyyar na kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya-bayan nan, wasu fitattun mambobin jam’iyyar adawa sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyun APC da ADC, ciki har da gwamnoni da ‘yan majalisa.
Me Makinde ya ce kan ficewa daga PDP?
Ya ce duk da cewa abubuwa na iya kama da suna ta tabarbarewa, jam’iyyar PDP za ta dawo kan turbar da ta dace nan ba da daɗewa ba, rahoton jaridar ThePunch ya tabbatar da labarin.
"Labarin da ke fita a yanzu shi ne mutane suna ficewa daga jam’iyya, gwamnoni suna sauya sheka."
"Amma ina da labari mai daɗi, lamarin yana iya zama kamar yana kara muni, amma a yawanci, idan ana son a gina abu mai ɗorewa, lamarin kan yi muni kafin ya gyaru.”
“Saboda haka, kada ku yi tunanin ko da na ɗan lokaci cewa ba za mu iya dawo da jam’iyyarmu kan hanya ba."
"Tun farkon wannan jamhuriya a 1999, PDP ta kasance ginshiki, ko dai a matsayin jam’iyyar da ke mulki ko kuma babbar jam’iyyar adawa tun daga 2015. Ba za mu je ko’ina ba.”
“Idan kun ji wasu sun sauya sheƙa, ku tsaya da kyau a PDP. Wannan lokaci ne da za a samar da sababbin jarumai na gaskiya, ba don PDP kaɗai ba, har da kasarmu baki ɗaya.”
“Wannan ba lokacin karaya ba ne, ba lokacin shakku ba ne. Wannan lokaci ne na nuna kwarin gwiwa."
- Seyi Makinde

Source: Facebook
Gwamna ya ba shugabannin PDP shawara
Makinde ya kuma yi kira ga dukkan shugabanni da mambobi su fifita ci gaban jam’iyya gaba ɗaya sama da muradunsu na kashin kansu.
Ya tabbatar da cewa shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na kasa da za a gudanar a watan Nuwamba suna tafiya yadda ya kamata.
'Dan majalisa ya yi murabus daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Sadiq Ango Abdullahi ya bayyana cewa ya yi murabus ne daga jam'iyyar PDP bayan ya dauki lokaci yana shawarwari.
'Dan majalisar ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na daga cikin dalilin da ya sanya ya raba gari da jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

