PDP Ta Sake Birkicewa, 'Dan Majalisa Ya Sanar da Murabus Dinsa daga Jam'iyyar

PDP Ta Sake Birkicewa, 'Dan Majalisa Ya Sanar da Murabus Dinsa daga Jam'iyyar

  • Matsala ta kara tunkaro jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya biyo bayan sake ficewar daya daga cikin mambobinta
  • 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Sabon Gari a jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya yi murabus daga jam'iyyar
  • Sadiq Ango ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na PDP na daga cikin dalilan da suka sanya ya yi murabus daga jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Jam'iyyar PDP ta kara rasa daya daga cikin 'yan majalisun da take da su a majalisar wakilai.

Dan majalisar wakilai , Hon. Sadiq Ango Abdullahi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP.

Dan majalisa ya fice daga PDP
Sadiq Ango Abdullahi. Hoto: Sadiq Ango Abdullahi
Source: Facebook

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na Facebook.

Meyasa Sadiq Ango ya fice daga PDP?

Sadiq Ango Abdullahi wanda ke wakiltar mazabar Sabon Gari a jihat Kaduna, ya ce rikice-rikicen cikin gida da rashin shugabanci a jam’iyyar ne suka tilasta masa yin murabus,

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta tsage gaskiya kan batun 'yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar

Ya bayyana cewa ya yi murabus din ne bayan dogon lokaci ana rikicin bangaranci, wanda ya ce ya hana shi yin aiki yadda ya kamata don jama’arsa.

Murabus ɗinsa ta zo jim kaɗan bayan tsohon sakataren jam’iyyar na kasa, S.K.E Udeh Okoye, ya yi murabus.

Sadiq Ango Abdullahi, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan kukumar kula da hanyoyi ta tarayya (FERMA), ya sanar da ficewarsa ne a cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban jam’iyyar a gundumarsa.

Sadiq Ango ya yi shawarwari kafin barin PDP

Ya bayyana cewa ya yanke shawarar ne bayan yin shawarwari da shugabanni da abokan siyasa, domin ci gaba da wakilci mai ma’ana da haɗin kai ga jama’ar Sabon Gari.

Sadiq Ango Abdullahi ya yi murabus daga PDP
Sadiq Ango Abdullahi a zauren majalisa. Hoto: Sadiq Ango Abdullahi
Source: Facebook
"Rikice-rikicen cikin gida da samun bangarori a jam’iyyar PDP, wanda ya janyo dogon rikici, sun yi tasiri wajen rage damar da nake da ita ta wakiltar mazabata da gudanar da aikina yadda ya dace."
“Ina godiya kwarai ga jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba ni na yi wa kasa hidima a karkashinta. Goyon baya da amincewa da gogewar da na samu a lokacin da nake cikin jam’iyyar ba za su taɓa ɓace mini ba."

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Kwamishinoni da manyan hadiman gwamna sun bar PDP sun koma APC

- Sadiq Ango Abdullahi

Ficewar Sadiq Ango Abdullahi da Udeh Okoye na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP ke fama da karuwar rashin jituwa a kan batun shugabanci da tsarin siyasa, musamman yayin da ake shirye-shiryen fuskantar zaɓe na gaba.

Gwamna Bala ya yi magana kan ficewa daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tabo batun raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa bai da wani shiri na ficewa daga jam'iyyar PDP wadda ya samu nasarar lashe zaben gwamna har sau biyu a karkashinta.

Bala Mohammed ya bada tabbacin cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar PDP, domin babu inda zai je.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng