2027: APC Ta Samu Matsala a Shirin da Ta So Yi a Jihohin Najeriya 36

2027: APC Ta Samu Matsala a Shirin da Ta So Yi a Jihohin Najeriya 36

  • Shirin rajistar mambobin jam’iyyar APC ta kwamfuta da aka kaddamar shekaru biyu da suka wuce bai ci gaba ba saboda rikice-rikice
  • An ce gwamnonin jam’iyyar ne suka karɓi ragamar aikin daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Umar Ganduje
  • Rahotanni sun yi hasashen cewa ana ganin cikas ɗin da ake cigaba da fuskanta yana da nasaba da shirye-shiryen siyasa da zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shekaru biyu bayan sanar da fara aikin rajistar mambobin jam’iyyar APC ta yanar gizo, har yanzu shirin bai samu nasarar farawa ba.

Wasu 'yan APC na ganin cewa rashin fara aikin ya samu cikas ne saboda rikice-rikicen cikin gida da canjin shugabanci a jam’iyyar.

Shugaban APC, Farfesa Yilwatda
Shugaban APC da wasu 'yan jam'iyyar a ofis. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnonin jam’iyyar ta hanyar kungiyar su ta PGF, karkashin jagorancin gwamnan Imo, Hope Uzodinma, sun karɓi ragamar aikin.

Kara karanta wannan

An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ganduje ya fara aikin a 2023

Dr. Abdullahi Ganduje, wanda tsohon gwamnan Kano ne, ya zama shugaban jam’iyyar na shida a watan Agusta, 2023.

A watan Satumba na shekarar, ya sanar da shirin rajistar mambobin APC ta yanar gizo domin ƙarfafa tsarin jam’iyyar kafin babban zabe mai zuwa.

Sai dai bayan wannan sanarwar fara shi, shirin rajistar yanar gizon bai ci gaba ba kamar yadda aka zata.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun alakanta tsaikon da rikice-rikice na cikin gida da kuma rashin daidaituwa tsakanin shugabancin jam’iyyar da gwamnonin.

Wani jigo a jam’iyyar, Barista Abdullahi Jalo, ya bayyana cewa

“An mayar da batun siyasa ne, kuma abin da ke faruwa yanzu duk game da shirye-shiryen 2027 ne.”

Rahoton FRCN ya nuna cewa Abdullahi Ganduje ya yi yunkurin fara shirin a farkon 2025 amma bai samu nasara ba.

Rikici tsakanin Gaduje da gwamnoni

Wani jami’in jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa ya yi zargin cewa rashin jituwa tsakanin gwamnonin APC Ganduje ne ya janyo tsaikon.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Gwamna ya tsallake da APC ta hana manyan 'yan siyasa 2 shiga takara

Ya ce:

“Ba a jitu kan yadda za a tafiyar da cibiyar ICT da ke kula da aikin ba. Gwamnoni sun ji cewa Ganduje yana gudanar da abin ba tare da tuntubar su ba, shi yasa suka kwace aikin.”

Sai dai wani na kusa da Ganduje ya musanta wannan zargi, yana mai cewa wasu gwamnonin ne suka gurgunta aikin saboda siyasa.

“Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya bayar da umarnin a fara rajista ta kwamfuta, Ganduje kuma ya fara aiwatarwa.
"Amma daga baya wasu suka janyo cikas saboda suna tsoron kada ya rage musu tasiri kafin 2027,”

- In ji shi.

Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje
Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje a wani taro. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Abin da ya kawo wa APC cikas a aikin

Wani shugaban yankin Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar APC, Alhaji Saleh Zazzaga, ya ce tsaikon ya biyo bayan sauyin shugabanci da kuma wasu matsaloli na cikin gida.

Wani ma’aikacin jam’iyyar a sakatariyar APC ya kara da cewa an fara shirye-shiryen horas da ma’aikata, amma komai ya tsaya cak.

Kara karanta wannan

Manyan APC sun kori shugabannin jam'iyya, an nada masu rikon kwarya a Enugu

Gwamna Mbah zai koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah yana shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC.

An bayyana cewa gwamnan zai sauya sheka ne tare da dukkan 'yan majalisar Enugu a matakin jiha da tarayya da kansiloli.

Shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC na jihar ne ya sanar da haka bayan kaddamar da shi a birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng