Tsohon Ministan Buhari Ya Tsage Gaskiya kan Shirin Ficewa daga APC
- Tsohon ministan sufuri a gwamnantin marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Muazu Sambo Jaji, ya yi magana kan barin APC
- Muazu Jaji Sambo ya nuna cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar APC domin bai da niyyar komawa wata jam'iyya daban
- Tsohon ministan ya bayyana cewa ya yi amanna da manufar gwamnati Shugaba Bola Tinubu wadda ya taimaka wajen kafuwarta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Tsohon Ministan sufuri a lokacin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Muazu Jaji Sambo, ya yi magana kan ficewa daga jam'iyyar APC.
Mu'azu Jaji Sambo ya bayyana cewa ba shi da niyyar barin jam’iyyar APC, inda ya ce zai ci gaba da kasancewa cikakkiyen ɗan jam’iyyar.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohon ministan ya bayyana hakan ne ta bakin mai taimaka masa na musamman kan yada labarai, Dr. Sam Idiagbonya.
Mu'azu Jaji Sambo ya jagoranci kamfen ɗin Tinubu/Shettima a jihar Taraba a zaɓen shekarar 2023.
Muazu Sambo ba zai bar APC ba
Mai taimakawa tsohon ministan ya bayyana cewa ubangidansa bai da shirin raba gari da jam'iyyar APC.
“Muazu Sambo Jaji ba zai je ko’ina ba; cikakken ɗan APC ne. Maigidana yana da cikakken imani da manufar Renewed Hope ta Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR), kuma yana da tabbacin cewa ba da daɗewa ba ‘yan Najeriya za su fara cin moriyarta.”
"Bayan ya jagoranci kamfen a 2023 wanda ya kawo wannan gwamnati, abin zai zama abin mamaki a ce yanzu zai sauya sheka. Sambo mutum ne mai biyayya da kishin kasa; ya na nan zai ci gaba da zama cikakken ɗan APC.”
- Dr. Sam Idiagbonya
Tsohon minista ya bukaci a goyi bayan Tinubu
Haka kuma, Dr. Sam Idiagbonya ya bayyana cewa tsohon ministan yana ganin jiharsa ta Taraba na da damar taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya da gwamnatin Tinubu ke kokarin ginawa ta hanyar noma.
Tsohon minisfan sufurin ya karfafa mazauna jihar Taraba da su ci gaba da nuna juriya da haɗin kai wajen gina sabuwar Taraba mai inganci da ci gaba.

Source: Facebook
Karanta karin wasu labaran kan jam'iyyar APC
- Abin da Tinubu ya ce ga 'yan PDP, ADC fiye da 60,000 da suka koma APC a Jigawa
- Gwamnoni 3 na shirin shiga APC, Gwamna Bala ya yi magana kan masu ficewa daga PDP
- Daga faduwa zaben cike gurbi, dan takarar jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC
Gwamna ya shirya komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Ndubuisi Mbah, ya shirya ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Gwamna Mbah ya shirya jagorantar 'yan siyasar jihar domin komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Mbah zai koma jam’iyyar APC tare da mambobin majalisun jiha da na tarayya 24, kansiloli 260, da kuma dukkan shugabannin PDP na jihar Enugu.
Asali: Legit.ng

