Al’umma Sun Fusata, Matasa Sun Farmaki Shugaban Karamar Hukuma a bainar Jama’a

Al’umma Sun Fusata, Matasa Sun Farmaki Shugaban Karamar Hukuma a bainar Jama’a

  • ‘Yan daba sun kai wa shugaban karamar hukuma hari yayin gudanar da aikin dakile cunkoson ababen hawa a titi wanda ya jawo rigima
  • An farmaki Hon. Osaro Eribo yayin tabbatar da bin ka'ida a karamar hukumar Egor ta jihar Edo a yau Lahadi 12 ga watan Oktoban 2025
  • Eribo ya bayyana cewa hakan ya faru ne bayan kamfanin sufuri na Muyi ya ƙi bin umarnin gwamnati kan ajiye motoci yadda ya kamata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Egor, Edo - Mutane sun fusata bayan shugaban karamar hukuma ya tako da kansa domin tabbatar bin ka'ida saboda rage cunkoso.

‘Yan daba sun kai wa shugaban karamar hukumar Egor hari yayin aikin hana cunkoson hanya a jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

An kai hari kan shugaban karamar hukuma a Edo
Gwamna Monday Okpebholo, Hon. Osaro Eribo. Hoto: @Osaro_osa_Eribo.
Source: Twitter

An farmaki shugaban karamar hukuma a Edo

Kara karanta wannan

Kebbi: 'Yan bindiga sun yi ta'asa bayan kai mummunan hari, sun fille kan Sarki

Shugaban riko na karamar hukumar Egor, Hon. Osaro Eribo ya tabbatar da faruwar hakan yayin hira da yan jaridu da Leadership ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eribo ya tsira daga harin ‘yan daba yayin da yake jagorantar aikin dakarar hana ajiye motoci barkatai da toshe hanya a yankin Uselu-Lagos.

Dan siyasar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da ya je duba korafe-korafen jama’a kan yadda direbobi ke ajiye motoci a ko’ina wanda ke haddasa cunkoso a hanya.

Ya ce tun farko majalisar karamar hukumar ta aika wa masu motoci da sanarwar gyara halayensu, amma sun ƙi bin umarni.

Ya ce:

“Tun da na hau kujerar shugabanci, kullum idan ina tafiya ofis sai in tarar da cunkoso a hanyar Muyi. Na je har ofishinsu na tattauna da manajan su, amma a ziyarar baya ya kore mu, daga nan ne wasu ‘yan daba suka kai mana hari."
Shugaban karamar hukuma ya magantu bayan kai masa hari
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudu maso Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Dalilin shirin rage cunkuso a Edo

Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa da ya ga hatsari yana neman faruwa, sai ya kira Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Jihar, wanda ya aika da ƙarin jami’an tsaro daga gidan gwamnati domin dakile rikicin.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Eribo ya bayyana cewa ba a yi aikin domin tsangwamar direbobi ko wani kamfani ba, sai dai don kare jama’a, cewar rahoton The Nation.

“Bayan ‘yan daban sun watse, mun kira shugabancin kamfanin Muyi zuwa ofishin majalisa domin su rattaba hannu kan takardar alkawari. Amma abin mamaki, su ne yanzu ke wallafa labaran ƙarya a kafafen sada zumunta suna juya gaskiya.
“Ba aikin muzgunawa ba ne, manufarmu ita ce tabbatar da tsaro da aminci ga jama’a. Ba za mu tsaya kallon rayukan mutane suna shiga haɗari kullum ba.”

Ya ƙara da cewa wannan aikin na cikin shirin gwamnati na tabbatar da cewa duk manyan tituna a Egor sun kasance cikin lafiya, masu bin doka da kuma rashin cunkoso.

Shugaban karamar hukuma ya suma a taro

A baya, kun ji cewa an shiga firgici da tashin hankali da shugaban karamar hukumar Bariga ta jihar Lagos, Kolade Alabi ya sume a wurin taron.

Kolade, wanda shi ne shugaban kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi (ALGON) ya yanke jiki ya faɗi a taron masu ruwa da tsakin APC a Lagos.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

An ruwaito cewa likitoci da hadimansa sun yi ƙoƙarin dawo da shi hayyacinsa kafin daga bisani aka garzaya da shi asibiti mafi kusa da sakatariyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.