An Zo Wajen: Gwamna Bala Ya Yi Magana kan Shirin Ficewa daga PDP

An Zo Wajen: Gwamna Bala Ya Yi Magana kan Shirin Ficewa daga PDP

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya tabo batun yiwuwar ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
  • Shugaban na kungiyar gwamnonin PDP, ya yi nuni da cewa ba za iya ficewa daga jam'iyyar ta adawa ba
  • Gwamna Bala ya nuna cewa akwai hannun wasu kan kokarin kawo rarrabuwar kawuna a jam'iyyar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Bala wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya bada tabbacin cewa ba zai raba gari da jam'iyyar ba.

Gwamna Bala ya ce ba zai bar PDP ba
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Gwamna Bala ya bada tabbacin ne wajen kaddamar da kwamitin sadarwa na babban taron PDP, ranar Asabar a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Bala ya ce kan ficewa daga PDP?

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya fadi abin da yake ji kan gwamnonin da ke ficewa daga PDP zuwa APC

Ya bayyana cewa ba zai ce takwarorinsa da suka bar PDP zuwa APC sun yi kuskure ba, amma shi dai ba zai fice daga jam'iyyar ba.

Gwamnan ya kara da cewa, wasu na barin jam’iyyar ne saboda lissafi da hasashe irin na siyasa, amma ya jaddada cewa shi ba zai bar PDP ba, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da labarin.

"Wani lokacin ana ficewa ne saboda lissafi irin na siyasa. Ba zan yi maganganu marasa kyau a kan takwarorina ba, amma ina bada tabbacin cewa ba zan je ko ina ba. Ina cikin PDP, kuma a jihata babu rarrabuwar kawuna."
"Ko a yau na gani a labarai cewa ɗaya daga cikin sanatocina zai tafi. Ana sarrafa su, ana siyan su, amma lallai jihata PDP ce."
"Jama’a na son canji, kuma sun yarda cewa canjin gaskiya zai fito ne ta PDP. Duk mafi yawan abubuwan da gwamnatin tarayya ke amfani da su a yau PDP ce ta kafa su.”

- Gwamna Bala Mohammed

Bala ya ba masu son barin PDP shawara

Gwamna Bala ya kuma bukaci wadanda ke shirin barin PDP da su yi hakan cikin lumana ba tare da bata sunan jam’iyyar ba, yana mai cewa fitarsu za ta buɗe kofar shigowar wasu sababbin hazikan ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya ce ga 'yan PDP, ADC fiye da 60,000 da suka koma APC a Jigawa

Ya bayyana fatan cewa babban taron jam’iyyar PDP mai zuwa zai samar da shugabanni nagari da za su iya kalubalantar APC tare da magance damuwar ‘yan kasa gabanin zaɓen 2027.

Gwamna Bala Mohammed ya ce zama daram a PDP
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a ofis. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Gwamna Bala ya ce ana kokarin lalata PDP

Da yake magana kan barazanar cikin gida daga wasu mambobin jam’iyyar, Gwamna Bala ya ce:

“Ba zan iya magana a madadin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ba, amma a matsayina na jagora a cikin jam’iyyar, na san suna bakin kokarinsu wajen magance matsalolin shari’a."
"Da yawa daga cikinsu an kirkire su ne don a lalata mu, amma babu rarrabuwar kai a cikin PDP.”

Dan takarar PDP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar jam'iyyar PDP a zaben cike na mazabar Kauran Namoda a jihar Zamfara, ya sauya sheka zuwa APC.

Mohammed Lawal ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC ne bayan shan kaye a zaɓen da aka gudanar a kwanakin baya.

Ya bayyana cewa bai ji daɗin yadda PDP ta yi watsi da shi bayan zaɓen ba, duk da irin gudunmawar da ya bayar a baya wajen samun nasarorin jam’iyya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng