Daga Faduwa Zaben Cike Gurbi, Dan Takarar Jam'iyyar PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC

Daga Faduwa Zaben Cike Gurbi, Dan Takarar Jam'iyyar PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Mohammed Lawal, tsohon ɗan takarar PDP a Zamfara, ya sauya sheƙa zuwa APC bayan ya zargi jam’iyyarsa da raina gudunmawarsa
  • Lawal ya ce APC tana da hangen nesa mai kyau, yayin da yaba da shugabancin Bello Matawalle, Abdulaziz Yari da Tukur Danfulani
  • APC ta bayyana karɓar Lawal a matsayin babban ci gaba, tare da fatan ƙarin manyan ‘yan siyasa za su bi sahunsa nan gaba kadan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara – Tsohon ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu, Mohammed Lawal, ya sanar da komawarsa APC bayan shan kaye a zaɓen.

Lawal ya bayyana matakinsa ne a ranar Asabar, yayin taron shawarwari na Yazeed Project da ya gudana a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamna na shirin komawa APC, tsohon jagora a Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

Dan takarar PDP a zaben cike gurbi a Zamfara ya sauya sheka zuwa APC
Gangamin da APC ta yi na karbar dan takarar PDP a zaben cike gurbi a Zamfara da ya sauya sheka. Hoto: @IbDanhausa
Source: Twitter

Zamfara: Dan takarar PDP ya koma APC

Ya bayyana cewa bai ji daɗin yadda PDP ta yi watsi da shi bayan zaɓen ba, duk da irin gudunmawar da ya bayar a baya wajen samun nasarorin jam’iyyar, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Dalilin da ya sa na bar PDP abu ne na kaina, amma ina tabbatar muku cewa Gwamna Dauda Lawal bai damu da jama’ar da suka yi masa aiki ba.”

Ya ce ya yanke shawarar komawa APC saboda hangen nesanta da manufarta mai kyau ga jama’a da ci gaban jihar.

APC ta yi maraba da dan takarar PDP

Mohammed Lawal ya bayyana cikakken yarda da shugabancin APC karkashin ministan tsaro, Bello Matawalle, tsohon gwamna Sanata Abdul’aziz Yari, da kuma shugaban jam’iyyar na jiha, Tukur Danfulani.

“Ina da tabbacin cewa APC ba za ta watsar da ni ba kamar yadda PDP ta yi, bayan na kashe kuɗi masu yawa domin ganin ta yi nasara a zaɓen 2023,” in ji Lawal.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Gwamna ya tsallake da APC ta hana manyan 'yan siyasa 2 shiga takara

Shugaban APC na jihar, Tukur Danfulani, wanda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris, ya wakilta, ya ce karɓar Lawal cikin jam’iyyar babban ci gaba ne ga APC a jihar.

“A madadin Ministan Tsaron Ƙasa Bello Matawalle da Sanata Abdul’aziz Yari, muna maraba da Mohammed Lawal cikin jam’iyyar APC. Wannan babbar nasara ce gare mu."

- Yusuf Idris.

Dan takarar PDP a zaben cike gurbi a Zamfara ya sauya sheka zuwa APC
Gangamin da APC ta yi na karbar dan takarar PDP a zaben cike gurbi a Zamfara da ya sauya sheka. Hoto: @IbDanhausa
Source: Twitter

Manyan ‘yan siyasa na shirin shiga APC

Yusuf ya ce Lawal ya yaba da yadda jama’a suka ba da goyon baya ga APC a lokacin zaɓen cike gurbi, kuma hakan ya nuna inda hankalin masu zaɓe ya karkata a jihar, inji The Punch.

Ya ƙara da cewa APC na sa ran karɓar ƙarin fitattun ‘yan siyasa cikin makonni masu zuwa, ciki har da ‘yan majalisar jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da jami’an PDP.

“Wannan farawa ne kawai, akwai sauran manyan shugabanni da za su biyo baya, za mu karɓe su hannu bibbiyu cikin APC."

- Yusuf Idris.

Dan takarar APC ya lashe zaben Kaura Namoda

Tun da fari, mun ruwaito cewa, dan takarar APC, Kamilu Sa’idu, ya lashe zaɓen cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Mutanen da suka ja junnen Jonathan game da sake neman mulkin Najeriya a 2027

Farfesa Lawal Sa’ad, jami’in tattara sakamako, ya bayyana sakamakon karshe da APC ta samu nasara a ranar Alhamis, 21 ga watan Agusta, 2025.

Hukumar INEC ta bayyana cewa APC ta lashe zaben da kuri’u 8,182, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Muhammad Lawal Kurya, ya samu kuri'u 5,543.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com